Bayar Da Lokaci

Lokaci

Daga cikin mafiya girman korafe-korafen da mata suke yi a kan mazajensu na aure, irin wadannan kalamai ba baki ba ne:

“Na tsani zaman majalisar nan da su ke yi kullum sai an raba dare.”
“Wai mutum shi da iyalinsa amma ba shi da lokacinsu, kullum ya gwammace zama a waje.
“Tsawon lokaci mutum ba shi da lokacinka, sai in bukatarsa ta kawo shi. Na tsani wannan abin.”
“Mutum kullum shi a aiki yake, mene amfanin aikin idan har ba zai bar ka ka samu lokacin iyalinka ba?”
“Na tabbata aiki da abokanka sun fi ni muhimmanci, tun da kullum a kan su lokutanka suke tafiya.
“Babu wani burge ni da duk wani kayan alatu zai yi, idan har ba ni da muhimmanci a wurin mutum.”
Abu guda kwakkwara kuma mafi muhimmanci da mutum zai yi saurin fahimta a cikin kafatanin korafe-korafen shi ne bukatar lokaci da matan suke yi daga wurin mazajensu. Kodayake, ba mata ne kadan suke fuskantar irin wannan matsala kuma su ke yin korafi shigen wadannan ba, sai dai kawai nasun ne ya fi yawa. Amma tabbas maza ma su kan fuskanci irin wadananan matsaloli.
Yayin da duk ka ji mutum korafinsa ya fi karkata ga irin wannan bukatu, na rashin samun lokaci daga abokin zamansa, to kai tsaye za ka iya cewa bayar da lokaci shi ne yarensa na soyayya.
Bayar Da Lokaci ba wai ya na nufin kasancewarku a zaune a wuri guda ba ne kawai. Bayan da lokaci yana nufin ma’aurata biyu su zauna tare da juna a wuri guda, ba aikin fari bare na baki. Su mayar da hankalinsu kacokan kan juna, ba tare da gayyatar ko yin wani abu da zai iya daukar hankalinsu ga barin juna ba. Kenan, zama ku kalli fim ko kwallo tare, ko ma duk wani abu da ya yi kama da wadannan.
Idan kuna tare, a zaune a wuri guda, amma kallon talbijin kuke yi. To wannan kallo kuke yi kenan, amma ba bayar da lokaci ga juna ba. A hannu guda kuma, idan ma a tafiye kuke, amma babu abin da kuke yi sai hira da juna. To wannan bayar da lokaci ne. A kalla dai, yanayin da za a iya kira na bayar da lokaci tsakanin ma’aurata ko masoya guda byu, dole ne ya kasance wani lokaci wanda ya ba su damar kadaita daga su sai su, kuma yak ore dukkan wani abu da zai iya dauke hankalinsu daga kan juna. Ko da kuwa a wannan lokacin ba sa ko hira da juna.
Wani abin sha’awa shi ne, a wuraren cin abinci ko na shakatawa ma ana iya gane ko bambance tsakanin mace da namijin da suka yi aure da kuma wadanda suke soyayya ko neman, kafin a kai ga yin auren. Domin yayin da su ma’aurata z aka taras idan suna zaune suna dan ciye-ciye ko shaye-shayensu, kalle-kalle suke ta yi. Ina nufin da wahala ka ga sun tsayar da hankalinsu wuri guda, sai dai kalli can su kalli wancan su kalli waccan. Yayin da su kuma wadanda suke kan ganiyar soyayyarsu, ba ma’aurata ba. Za ka taras duk sun tattara hankalinsu wuri guda, a kan junansu. Hirarsu ya su ya su, kuma idanuwansu ma suna kan juna. Irin wannan yanayi shi ne kuma ainishin yanayin da ake so a samu a yayin da aka ambaci bayar da lokaci.
Yayin da ka zauna da matarka na a kalla misalign mintuwa goma sha biyar, kuma ya kasance don ita kawai ka zauna, babu wani abu da kake yi sai kallo da sauraren ta. Ita ma kuma ta kasance a cikin irin wannan hali. To kamar kun sadaukar da wadannan mintuna ne ga juna. Domin wannan lokacin ya shude kenan, ba zai taba dawowa ba. Sai dai abu mafi muhimmanci shi ne, wannan zaman zai kara zama wani sanadin samar da farin ciki da karfafa gwiwar juna a tsakaninku.
Wannan zama, harwayau, wani ciniki ne mai gwaggwabar riba, wanda idan ka bar shi zai yi wuya ka iya aikata wani ciniki da ya kai shi riba a lokacin, ko da kuwa mai za ka yi. Domin hadisi ya tabbbata daga Annabi sallallahu alaihi wa sallam cewa, zamanka da iyalinka na sa’a guda ya fi ka tafi itikafi a masallacin Madina! Lallai idan z aka tsaya ka lissafa girman wannan ladan, to mamaki zai cika ka, kuma z aka yarda cewa ko da dai babu komai, kuma ko da bayar da lokaci bay a kara soyayya a tsakaninka da iyali, to ya kamata ka lizimce shi a matsayin ibada.
Abin mamaki shi ne yadda muke zabar zaman majalisun hira, wadanda yawanci zaman su yake saurin bayuwa ga daukar alhaki. Mu yi watsi da wannan aiki mai cike da nishadi da kuma lada.
Kodayake, daga matsalolin da ma’aurata suke fama da su, wadanda kuma suke haddasa hana bayar da irin wannan lokaci, akwai matsalar rashin iya hira. Daga abubuwan da na sha ji, wanda kuma na tabbata mutane da yawan gaske ne suka amince da shi, akwai batun da maza suke yi cewa in ma kana son zaman lafiya da mace to kar ka yawaita zaman hira da ita. Jin wannan kuma ba wani abin mamaki ba ne, idan an yi la’akari da irin girman bambance-bambancen da suke tsakanin mata da mazan wurin fahimtar al’amura. Wanda masana sun yarda cewa tamkar yare ma kusan kowannne da irin nasa. Wato sau da dama maza za su fadi magana mata su yi mata wata fahimtar ko fassarar daban. Kamar kuma haka su ma a nasu bangaren suke yi wa tasu maganar.
Wannan lamari ya taka muhimmiyar rawa kwarai wurin hana ma’aurata tsawaita zama tare. Kuma shi ya sa a can baya muka taba kawo wasu muhimman darusa guda biyu, wadanna za su taimaka mana wurin nakaltar yadda za mu rika hira tsakaninmu da juna. Na farko shi ne darasin da muka yi na kamusun Da Yake Fassara Maganganun Mata sai kuma na biyu wai taken Yadda Ake Sauraren Mace, harwayau, darasin da muka yi mai taken Wayayyun Ma’aurata zai taimaka gaya a wannan fanni.
Abu ne mai muhimmanci kwarai ga duk wadda ko wanda yake samun matsala ta rashin fahimta yayin tattaunawa ga iyali, ya koma baya ya kara nazarin wadancan darussa guda uku. Wadanda a kalla muke sa ran mai karatu zai iya fahimtar cewa, mata sau da yawa suna yin magana ne kamar irin ta mawaka, mai hashen damo. Shi ya sa kai sai ka fahimce ta da wata ma’anar daban, alhali ita kuma wani abu daban take nufi. Wannan kuma shi ya sa wataran in kuna magana da mace, sai ka ji tana ce maka “Kai b aka ganewa.” Sannan za ka iya fahimtar yadda suke hirarsu, da yadda suke son a rika bin su yayin da suke magana. Ina ne ya kamata ka yi magana, ina ne kuma ya kamata ka gyada kai da kuma inda ya kamata ka yi shiru ma. Haka nan, z aka iya fahimtar ashe ba kullum ne idan mace ta tada jijiyar wuya tana suruta yayin da take yin magana da kai, kai din take jin haushi ba.
To idan har za mu iya tuna irin wadancan batutuwan, za mu taras samun damar amfanar bayar da lokaci tsakaninmu, ba zai zama wani tashin hankali ba. In sha Allah.

Exit mobile version