Bayelsa: Matashi Ya Kashe Abokin Takararsa Wajen Budurwa

Wani matashi mai suna Eyor Eketen dan shekara 35 da haihuwa, ya kashe abokin takararsa wajen neman aure mai suna Charles a garin Yenagoa cikin Jihar Bayelsa. An bayyana cewa, Eketan ya soke mutumai har lahira a gidan su budurwansa da ke kan titin Nikton cikin yankin Kpansia. Charles ya bar iyalansa cikin zullumi, inda ya tafi kan titin Nikkton ba tare da sanin ajalinsa ya zo karshe ba.

Budurwar mai suna Lobina Okon ‘yar asalin Jihar Akwa Ibom, ita ce ta bayyana wa wani makwabcinta cewa, saurayinta ya kashe bakon ta mai suna Charles. Nan take makwabcin ya zo dakinta da gudu, inda ya tarar da Charles kwance cikin jini.

Wani wanda lamarinm ya faru a gaban idanunsa ya bayyana cewa, “makwabta sun ga wanda ya aikata wannan mummunan lamari da kuma wanda aka soke kwance cikin jini. Mutane sun yi ihun neman taimako. “’Yan sanda sun zo sun tafi da wanan mutumin da ya kashe mamacin mai suna Eyor Eketen dan shekara 35 da haihuwa. Ya dai aikata wannan kisan ne a garin Yenagoa babban birnin Jihar Bayelsa.

 

Exit mobile version