Umar A Hunkuyi" />

Bayelsa: Sylba Ya Nemi Gafarar Buhari Da Aisha

Karamin Minista a Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylba, ya bai wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da mai dakinsa Hajiya Aisha Buhari hakuri a kan yadda shirinsu na halartar rantsar da Dabid Lyon na jam’iyyar APC a matsayin gwamnan Jihar Bayelsa ya sami cikas sakamakon hukuncin da Kotun Koli ta yanke, inda ta rusa zaben nashi.

Sylba ya ce, “bayar da hakurin ya zama tilas sabili da ya na sane da irin shirin da Shugaban Kasar, Uwargidansa Aisha da manyan jami’an fadar gwamnatin ta tarayya su ka yi shirin isa birnin Yenogoa, domin halartar bikin rantsar da Lyon din a ranar Juma’ar da ta gabata.”

Timipre Sylba, wanda shi ma tsohon gwamnan Jihar ta Bayelsa ne, ya kwatanta lamarin da cewa, “dan tsaikon da a ka samu,” wanda hukuncin Kotun Kolin ya yi umarni da a rantsar da Douye Diri na Jam’iyyar PDP a matsayin sabon Gwamnan Jihar ta Bayelsa.

Ya kuma yi kira ga daukacin ’ya’yan jam’iyyar ta APC a Jihar da kada su dauki doka a hannunsu, domin shugabannin Jam’iyyar a Jihar suna wani yunkuri tare da Lauyoyi domin nasarar hukuncin da kotun ta yanke.

Ya kuma sake nanata tabbaci ga Shugaba Buhari da shugabannin Jam’iyyar na kasa cewa, lallai Jam’iyyar ta APC a Jihar ta Bayelsa ta na nan daram da karfinta.

“Ina kuma kara jaddada yin kira ga al’ummar Jihar Bayelsa da su manta da duk wani bambance-bambance a tsakaninsu, su kuma guji tayar da hargitsi ko da kuwa wane irin mataki na tsaro ne za a dauka a kansu,” a cewarsa.

Hukuncin dai na Kotun Koli, wanda ta yanke, da kuma rantsar da Duoye da a ka yi a ranar Juma’ar da ta gabata ya janyo yunkurin haddasa fitina daga wasu zauna gari banza, inda har su ka fara far wa kayayyakin al’umma da gidajen mutane, kamar gidan tsohon gwamnan Jihar Dickson da na sabon gwamnan Jihar, Diri.

Exit mobile version