Abba Ibrahim Wada" />

Bayern Munchen Ta Na Son Biyan Kudin Griezman

Wasu rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen ta shirya biya kudin dan wasan Atletico Madrid, Antonio Griezman domin ya koma kungiyar a kakar wasa mai zuwa.
Griezman mai shekara 28 a duniya tauraruwarsa tana haskawa a wanann kakar wasan bayan daya zura kwallaye 20 cikin wasanni 43 daya bugawa kungiyar kuma sune a matsayi na biyu a gasar cin kofin laliga da ake bugawa.
Farashin dan wanda kungiyarsa ta Atletico tayi masa shine fam miliyan 200 sai dai a karshen watan Yunin wannan shekarar farashin zai koma fam miliayn 129 kamar yadda rahotanni suka bayyana daga kasar Sipaniyan.
Tuni dai shirye shirye sukayi nisa a kungiyar ta Bayern Munchen domin kashe makudan kudade domin kakar wasa mai zuwa kuma dan wasa Griezman yana daya daga cikin ‘yan wasan da suke ganin zai kara musu karfi idan suka siyeshi.
A kakar wasan data gabata kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ce ta kusa siyan dan wasan sai dai daga baya kuma yaki amincewa da barin kungiyarsa inda ya sake sabon kwantaragi dab da za’a fara gasar cin kofin duniyar da suka lashe a kasar Rasha.
Tuni daman dai Munich ta siyi takwaransa na Atletico Madrid Din kuma shima dan kasar Faransa, Lucas Harnandez, wanda zai koma kasar ta Jamus da buga wasa a sabuwar kakar wasa mai zuwa da za’a shiga.

Exit mobile version