Bayern Munich Ta Lallasa Tottenham 7 Da 2 A Gasar Zakarun Turai

Tsohon matashin dan wasan Arsenal Serge Gnabry ya kafa tarihi da cin kwallaye hudu bayan hutun rabin lokaci a gasar Zakarun Turai ta Champions League

Lissafi ya ci gaba da dame wa Tottenham bayan da bakinta ‘yan Bayern Munich suka kunyata ta da ci 7-0 a gasar Zakarun Turai ta Champions League.

A karawar ta Talata da daddare, girma-girma Tottenham ta fara wasan da kuzari har Son Heung-Min ya fara ci mata bal a minti na 12.

Bayan nan ne kuma fa sai wasa ya sauya salo minti uku tsakani murna ta koma ciki Joshua Kimmich, ya farke wa bakin.

Ana dab da tafiya hutun rabin lokaci ner kuma sai Robert Lewandowski ya kwarara wa golan Tottenham, Hugo Lloris wata bal din daga tazarar yadi 20, ba ta zame ko ina ba sai a raga.

Dawowa daga hutun rabin lokaci ne kuma sai lissafi ya kara cabewa Tottenham, inda Serge Gnabry ya rika daga musu raga ba a jere a jere.

Wannan ne ci mafi yawa da aka taba yi wa wata kungiyar Ingila a gida a duk wata gasar Turai

A minti na 53 da na 55, wato minti biyu tsakani ya jefa bal biyu.

Daga nan sai Harry Kane ya dan lasa wa Tottenham a minti na 61 amma da bugun fanareti, ta samu ta biyunta kuma ta karshe kenan.

Wasa ya yi nisa a minti na an kusa tashi a minti na 83 da kuma na 88, Gnabry ya sake yi wa masu masaukinsu kata’i da bal ta shida da kuma ta bakwai.

Wannan ciye-ciye da tsohon dan wasan na Arsenal , Gnabry ya yi, ya zama dan wasa na farko a tarihin gasar ta Zakarun Turai da ya ci bal hudu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Dodon-raga, Serge Gnabry ya ci yawan kwallo daidai da Harry Kane a filin wasan Tottenham

A tarihi ba wata kungiyar kwallon kafa ta Ingila da aka taba ci da yawa haka a gida a duk wata gasar Turai.

Wannan kuma shi ne karon farko a tarihin kungiyar Tottenham na shekara 137 da kafawa da aka ci ta kwallo bakwai a gida a duk wata gasa.

Yanzu dai ana ganin an shiga wani lokaci da kungiyar za ta sake nazarin zama da kociyanta Mauricio Pochettino, ganin irin halin kunyata da take kara shiga a bana.

Har yanzu a aikinsa na kociya na shekara goma Mauricio Pochettino bai dauki kofi ba

A wasannin kungiyoyin biyu na gaba Tottenham za ta ziyarci Brighton a gasar Premier ranar Asabar da rana.

Ita kuwa Bayern da ke ta daya a gasar Bundesliga ta Jamus za ta kasance ne a gida da Hoffenheim a ranar Asabar din.

Exit mobile version