Abdulrazaq Yahuza Jere" />

BBC Hausa Zai Rufe Gasar Hikayata Ranar Lahadi Mai Zuwa

Daga Abdulrazaq Yahuza Jere

Za a rufe gasar Hikayata ta rubuta gajerun labarai ta bana da Sashen Hausa na BBC yake shiryawa, ranar Lahadi mai zuwa, 22 ga Agustan 2021 idan Allah ya kai mu.
Sashen Hausa na BBC ne ya ƙiƙiro da gasar rubuta gajerun labaran a shekara ta 2016, domin ƙarfafa wa mata gwiwar bayyana labaran abubuwan da suka shafe su.
Sanarwar da Jami’ar yaɗa labarai ta BBC mai kula da ɓangaren Afirka, Marina ta aike wa LEADERSHIP Hausa ta bayyana cewa gasar tana maraba da rubuce-rubucen hikaya ta mata cikin harshen Hausa a kalmomin da suke tsakanin 1000 zuwa 1500.
Sanarwar ta ce ga duk mai neman ƙarin bayani a game da sauran ƙa’idojin gasar ya leƙa shafin intanet na Sashen Hausa na BBC a adireshin: bbchausa.com, a duk lokacin da aka buɗe gasar.
Wata tawagar alƙalan gasar ce dai za ta zaɓi wacce ta lashe gasar, da kuma mutum biyu da ke bi mata har zuwa kan sauran waɗanda suka nuna bajinta a gasar.
Da yake tsokaci, Editan Labarai na Sashen Hausa na BBC, Aliyu Tanko ya ce: “Mun samu gagarumar nasara a gasar, tun daga lokacin da aka kafa ta shekara shida da suka gabata. Hikayata ta bai wa mata da yawa damar faɗar albarkacin bakinsu, mafi a’ala shi ne ta zama wani fage da suke nuna tsagwaron basirar da suke da ita. A bara mun samu mata 400 da suka shiga gasar a duniya kuma a bana muna sa ran yawan za ta fi haka.”
A nashi ɓangaren, Shugaban Sashen Harsunan Afirka ta Yamma na BBC, Oluwatoyosi Ogunseye ya ce: “Na yi farin ciki da muka sake shirya gasar Hikayata. Masu sauraro mata na samun matuƙar kulawa a cikin abubuwan da BBC yake aiwatarwa kuma za mu cigaba da ba da goyon baya ga gasar rubutun. Masu sauraronmu a sashen Hausa na da matuƙar daraja a wurinmu waɗanda suka yi amannar cigaba da sauraron BBC.
“Yana da matuƙar jin daɗi ka ga yadda rayuwar marubutun ke samun sauyi tun daga shiga gasar kuma shi ya sa yake da muhimmanci ka zaƙulo marubuta mata.”
A bara dai wata matashiya mai shekara 20 a duniya, ɗaliba a fannin nazarin shari’a daga Sakkwato, Maryam Umar ce ta lashe gasar da gajeren labarinta mai taken “Rai da Cuta”, wanda a ciki ta bayar da labarin wata mata mai ɗauke da juna biyu, Azima wacce mijinta ya shafa mata cutar Korona, lamarin da ya janyo rasa ɗan da ke cikinta da kai ta gargarar mutuwa.
Maryam dai ta ce nasarar da ta samu a gasar ta buɗe mata sabon babi a rayuwa da kuma zama miloniya.
Idan ba a manta ba, gasar Hikayata ta farko wani labari game da uƙubar da ‘yan gudun hijirar yaƙin Boko Haram mai taken “Sansanin ‘Yan Gudun Hijira” ne ya lashe.

Har yanzu dai ana cigaba da karɓar gajerun labarai na shiga gasar ta adireshin: labari.bbchausa@bbc.co.uk wanda ake sa ran rufewa a ranar 22 ga Agustan 2021.

Sanarwar da BBC ya fitar ta ce masu sauraro za su iya sauraron labaran da aka zaɓa aka darje a gasar, nan da ‘yan watanni masu zuwa.
Za a gabatar da kyaututtuka na kuɗi da lambobin yabo ga gwarzuwa da masu bi mata su biyu a wata walima da za a shirya a watan Nuwamba idan Allah ya kai mu.

 

Exit mobile version