Rabiu Ali Indabawa" />

Benezuela Ta Rufe Ofishoshin Jakadanci Da Ke Canada

Kasar Benezuela ta sanar da aniyar ta na rufe kananan ofishoshin jakadancin kasar dake kasar Canada biyo bayan matakin hukumomin Canada na rufe ofishin jakadancin kasar dake birnin Caracas.
Gwamnatin Benezuela ta bayyana cewa a duk fadin kasar ta Canada, ofishin jakadancin ta daya cillo dake birnin Ottawa zai ci gaba da aikin sa.
Mako daya kenan da hukumomin Canada suka dau matakin rufe ofishin jakadancin su,bisa dalilan cewa Shugaban kasar Nicolas Maduro ya hanawa wasu jakadun Canada takardun aiki a kasar.
Matakin rufe ofishoshin jakadancin Benezuela a Canada na zuwa ne a wani lokaci da kasashen Duniya ke ci gaba da kira zuwa Shugaba Maduro na kawo sassauci ga shugabancin sa.

Exit mobile version