Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Benin: Wani Mutum Ya Kashe Surukansa Uku Saboda Tsananin Zalunci

by
3 years ago
in Tauraruwa Mai Wutsiya
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Rundunar ‘yan sandar Jihar Edo ta samu nasarar damke Edogho Omorogbe dan shekara 44, diraban tifa ne, bisa laifin kashe mahaifiyar budurwarsa mai matarsa Alice Omorogbe ‘yar shekara 52, yayar matarsa mai suna Blessing Efe ‘yar shekara 25 da kuma kanuwarsu jiririya ‘yar wata shida. Omorogbe ya na daya daga cikin wadanda a ke zargi guda 100, wanda kwamishinan ‘yan sandar jihar, Dan Mallam Muhammed ya gurfanar da su, bisa aikata laifuka daban-daban a cikin jihar.

Shi dai Omorogbe ya kashe iyalan ne a ranar 10 ga watan Satumba, a gidansu da ke yankin Iguadolor cikin karamar hukumar Obia ta arewa maso gabas ta jihar.

A cewarsa, an gano gawar jaririyar ce bayan kwana daya da kisan. Ya kara da cewa, a lokacin wannan farmaki akwai yarinya ‘yar shekara biyu a cikin dakin, amma yarinyar ta tsallake rijiya da baya. Ya ce, za a gurfanar da wanda a ke zargi a gaban kotu nan ba da jimawa ba.

Labarai Masu Nasaba

Waiwayen Kanun Labarai Daga Litinin 15 Zuwa 18 Ga Sha’aban 1442 Bayan Hijira

’Yan Sanda Sun Gabatar Da Masu Manyan Laifuka 17 A Jos

Da ya ke zantawa da manema labarai, shi wanda a ke zargi ya bayyana cewa, ya kashe mutanen ne saboda su na yin hayar matasa  su na bugun sa duk lokacin da su ka samu rashin jituwa shi da matarsa. “Na kashe su ne cikin fushi, saboda mahaifiyar matana ta na turo matasa su buge ni. Na samu rauni a gefen idona na hagu sakamakon wani hari da su ka taba kai mun. Duk lokacin da na ke da wata matsala da matana, sai mahaifiyarta ta ce ya na ke rike matana ta hanyar da bai dace ba. Idan mu ka yi fada da matana, sai ta turo min matasa su buge ni. “Lokacin da na je gidan, sai na tarar an rufe kofa, sai na tsallaka cikin gidan sannan na kashe su da adda. Bai yi nayyar kashe jaririyar ba, ban san lokacin da adda ya taba ta ba,” in ji shi.

Ya kara da cewa, bayan ya kashe mamatan, ya yi kokarin bayewa, amma sai ya ga labarin a talabijin, inda daga baya  a ka damke shi. “Lokacin da na je gida, sai mahaifina ya tambaye ni a kan ko dai ni ne na aikata wannan laifi. Sai na bayyana masa cewa, ni ne na aikata, domin babu abinda zan iya boye masa. Ya kira ‘yan sanda, inda su ka cafke ni.”

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

‘Yan Bindiga Sun Halaka Mutum Biyu Har Lahira A Ribas

Next Post

An Nemi ’Yan Agajin Izala Su Rungumi Ilimi Da Sana’o’i

Labarai Masu Nasaba

Labarai

Waiwayen Kanun Labarai Daga Litinin 15 Zuwa 18 Ga Sha’aban 1442 Bayan Hijira

by
1 year ago
0

...

’Yan Sanda Sun Gabatar Da Masu Manyan Laifuka 17 A Jos

by
3 years ago
0

...

Wata Mata Ta Kwace Jariri Daga Hannun Mahaifiyarsa A Ekiti

by
3 years ago
0

...

‘Yan Bindiga Sun Halaka Mutum Biyu Har Lahira A Ribas

by
3 years ago
0

...

Next Post

An Nemi ’Yan Agajin Izala Su Rungumi Ilimi Da Sana’o’i

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: