Dan wasan Manchester City Benjamin Mendy zai je wani asibitin kwararru a birnin Barcelona na kasar Spain, bayan raunin da ya ji a gwiwa a wasansu da Crystal Palace.
An sauya Mandy ne a minti na 29 a wasan da suka doke Crystal Palace da ci 5-0 a ranar Asabar.
Da yake magana game da batun da farko, kocin kungiyar Pep Guardiola ya ce yana ganin dan kwallon zai koma atisaye ne a ranar Litinin.
Sai dai ba a ga dan wasan a lokacin atisayen.
Ramon Cugat ne zai yi wa Mandy magani, wato likitan da ya taba yi wa Bincent Kompany da Kebin de Bruyne magani a kakar bara.