Beraye Sun Fatattaki Wasu Fursunoni Da Ma’aikata Daga Gidan Yari

Beraye

Wasu beraye sun addabi wani gidan yarin kasar Australia, lamarin da ya kai ga kwashe fursunonin gidan. Berayen sun addabi gidan yarin ne tare da barnata wurare da dama na gidan cikin kankanin lokaci.

Hukumar gidan yarin ta bayyana cewa, za ta gudanar da gyara kafin daga bisani a dawo da fursunonin.

A wani rahoto da jaridar The Guardian ta ruwaito, wasu beraye sun tilasta kwashe fursunoni daga wani gidan yari a kasar Australia bayan sun addabe su. Sama da fursunoni 400 ne da ma’aikata 200 na gidan yarin Wellington a New South Wales aka sauya wa matsuguni na tsawon mako biyu kafin a yi maganin berayen. Berayen sun yi barna sosai inda suka lalata gidan yarin da kuma cin wayar wuta.

Yankin ya dade yana fama da matsalar beraye, wannan kuma ya sa za a rage yawan mazauna gidan yarin zuwa tsawon wata hudu.

Kwamishinan kula da fursunoni na NSW, Peter Seberin, ya ce za a rage ayyukan a kurkukun ne don magance barnar berayen, kuma an dakatar da ziyarar cikin-gida har sai aikin gyaran ya kammala.

A ranar Talata, Mista Seberin ya ce: “Lafiya, aminci da walwala na ma’aikata da fursunonin shi ne babban fifiko na farko saboda haka yana da muhimmanci a gare mu mu yi aiki a yanzu don aiwatar da gyara.” “Muna bukatar daukar wannan matakin a yanzu don tabbatar da tsaftace gidan da kuma gyara kayayyakin more rayuwa.

Exit mobile version