Tare da Sani Anwar 08036365416 (leadershipayau.com)
Shugaban Amurka da takwaransa na kasar Koriya ta kudu na kiran a kara sanyawa koriya ta arewa takunkumi. kasashen China da Rasha, dake manyan kawayen Koriya ta arewa, sun ce kiraye-kirayen da ake yi na kara zafafa takunkumi akan Koriya ta arewa bayan gwajin makamin Nukiliyar da ta yi na baya-baya ba zai taimaka ba sosai wajen rage fargaban da ake fama da shi a mashigen koriyoyin biyu.
Da ya ke magana a wajen taron kolin kasashen Brazil, Rasha, da Indiya, da kuma China, na kasashe masu bunkasar tattalin arziki da ake yi a birnin Diamen na kasar China, shugaban Rasha Bladimir Putin yayi Allah Wadai da gwajin makami mai linzamin da Koriya ta arewa tayi na baya-baya, amma yayi gargadin cewa ruruta wutar daukan matakin soja zai iya haddasa bala’i a duniya.”
Putin ya kuma caccaki Amurka akan kiran da ta yi na a kara sanyawa Koriya ta Arewa takunkumi. Ya kira matakin “Mara amfani wanda kuma ba zai yi aiki ba”. Ya kara da cewa shashanci ne Amurka ta sanyawa Rasha takunkumi saboda tana kasuwanci da Koriya ta arewa, kuma daga baya ta dawo tana neman Rasha ta taimaka ta sanyawa yanken da aka maida saniyar ware takunkumi.