Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home KASASHEN WAJE

Biden Na Shirin Gabatar Da Jami’an Da Zai Nada a Gwamnatinsa

by Muhammad
November 26, 2020
in KASASHEN WAJE
2 min read
Gwamnatinsa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Rabiu Ali Indabawa

Zababben shugaban Amurka Joe Biden zai yi wani taro a yau Talata domin gabatar da mutanen da yake so ya zaba don rike manyan mukamai na diplomasiyya da na tsaron kasa a gwamnatinsa. Daga cikinsu a akwai Antony Blinken, daya daga cikin makusantan Biden a tsakanin masu ba shi shawara kan harkokin kasashen waje – wanda shi ake sa ran zai rike mukamin Sakataren Harkokin wajen Amurka.

samndaads

Biden ya kuma ce yana da niyyar daukan tsohon sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry domin rike sabon mukamin wakilin shugaban kasa na musamman kan yanayi, yayin da zai kuma rike wani mukami a Majalisar tsaron Kasa. Hakan, mataki ne da ke nuna yadda shugaban mai jiran-gado zai mayar da hankali kan yadda za a tunkari batun sauyin yanayi a matsayin batu na gaggawa a cewar tawagar karbar mulkin Biden.

Wannan na faruwa ne yayin da hukumar da ke kula da ayyukan tafiyar da mulki a nan Amurka, ta amince cewa Biden ya cancanci a ba shi duk hadin kan da yake bukata bisa tanadin da dokar 1964 ta yi, don a samu damar mika mulki ba tare da wata tangarda ba. A tsakanin yanzu zuwa ranar 20 ga watan Janairu da za a rantsar da shi, Biden zai ci gaba da nade-naden mukamai a gwamnatinsa na jami’an da za su aiwatar da manufofinsa, idan ya karbi ragamar mulki – ya kuma samu damar tafiyar da fannin tsaron kasa.

SendShareTweetShare
Previous Post

Tsohon Shugaban Jamhuriyar Nijar Tandja Mamadou Ya Rasu

Next Post

Gwamnatin Gombe Za Ta Shawo Kan Matsalolin Da Sansanin NYSC Ke Fuskanta A Jihar

RelatedPosts

Faduwar Trump

Me Zai Biyo Bayan Darewar Karajar Biden Da Faduwar Trump?

by Muhammad
2 days ago
0

Idanun duniya na kan ranar Larabar jiya, 20 ga Janarairu,...

Allurar Korona

An Soma Yin Allurar Korona A India Da Brazil

by Muhammad
2 days ago
0

A yau asabar kasashen Duniya da suka hada Indiya ,Brazil...

Trump Ya Fice Daga Fadar ‘White House’ Gabanin Rantsar Da Biden

Trump Ya Fice Daga Fadar ‘White House’ Gabanin Rantsar Da Biden

by Muhammad
2 days ago
0

Trump ya ce mutane "ba su san aiki tukuru" da...

Next Post
Sansanin NYSC

Gwamnatin Gombe Za Ta Shawo Kan Matsalolin Da Sansanin NYSC Ke Fuskanta A Jihar

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version