Zababben shugaban Amurka Joe Biden ya gabatarwa Amurkawa shirinsa na tabbatar da cewa dukkansu sun samu rigakafin cutar Korona yayin da ake ci gaba da samun sabbin mutanen da ke kamuwa.
Biden wanda ake sa ran rantsarwa ranar Laraba mai zuwa, ya ce abin da zai sanya a gaba da farko shine ganin cewa an yi wa duk wanda ya haura shekara 60 a duniya rigakafin cikin gaggawa.
Sannan ya ce gwamnatinsa, za ta yi aiki kafada da kafada da gwamnatocin jihohi domin bude karin cibiyoyin yi wa mutane rigakafi.
Mista Biden ya ce ya yi imanin cewa a shirye Amurkawa suke su bawa gwamnati hadin kai don yaki da annobar.