Ramadan: Sakonnin ‘Yan Fim Din Hausa Ga Duniyar Musulmi

Daga  Aliyu Ahmad

A yayin da Musulmi a fadin duniya ke nuna farin cikinsu game da sake zagayowar watan Azumin Ramadan, wasu daga cikin fitattun jaruman finafinan Kannywood sun mika sakonnin fatan alheri da zagayowar watan na Ramadan ga Musulmin duniya, musamman masoyansu a fagen fim. Wakilinmu ya dan tattaro wasu daga cikin sakonnin kaar haka:

 

Ina mai farin ciki da Allah ya sa muka kasance daga cikin wadanda suka sake ganin zagayowar wannan wata mai albarka. Ina fatan Allah ya sada mu da alherin dake cikinsa.

Sannan zan yi kira ga al’ummar Musulmi da su dage da addu’o’i domin ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan. Sannan kuma mu dage da ibadu don samun rabon dake cikin wannan wata.

 

Da farko ina mai taya ‘yan’uwa Musulmi murnar zagayowar wannan wata na Ramadan, wanda wata ne mai albarka. Ina fatan Allah ya sada mu da alkairan dake cikinsa, ya kuma sa muna daga cikin ‘yantattun bayi na wannan wata.

Zan ku ma yi kira ga al’ummar Musulmi musamman na Nijeriya da mu dage da addu’a wajen ganin kasar nan ta samu ci gaba da zaman lafiya mai dorewa. Allah ya amshi ibadunmu amin.

 

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki da ya sake nuna mana wannan wata mai albarka, wato Ramadan, wanda dukkan musulmi yana farin cikin da zagayowarsa.  Ina fatan ‘yan uwa Musulmi za su dage da ibada don ganin sun kasance daga cikin bayin da za su rabauta kasancewar wata ne na ‘yanta bayi.

Sannan kuma wata ne da ake rufa kofar wuta a bude ta Aljanna, wanda hakan wata dama ce na samun rahma cikin sauki ga Musulmai, don haka kada mu yi watsi da wannan dama a matsayinmu na wadanda suka yi imani da Allah da Manzonsa.

Allah ya karbi ibadunmu, Allah kuma ya sa mu kammala ibadun wannan wata mai alfarma cikin sa’a, ya kuma nuna mana na badin-badada.

 

Ina taya ‘yan’uwana Musulmi murnar zagayowar wannan wata na Ramadan. Allah ya sa mu kammala azumi cikin sa’a, ya sa kuma muna daga cikin wadanda za su rabauta da garabasar dake cikin wannan wata. A sha ruwa lafiya.

 

Da farko ina mai godiya ga Allah da ya nuna mana wannan wata mai albarka. Ramadan wata ne da ya kasance mai albarka ga ‘yan uwa musulmi, wanda Allah yake ‘yanta bayinsa a cikinsa. Ina fatan Allah ya sa muna daga cikin wadanda Allah zai ‘yanta a wannan wata mai albarka.  Domin watan Ramada wata dama ce da duk wani Musulmi zai iya amfani da ita domin neman rahmar Allah. Don haka kada mu sake wajen yin ibadu da gudanar da ayyukan alkairi.

Allah ya amshi ibadunmu. Ya kuma sada da alherin da ke cikin wannan wata mai alfarma.

 

To da farko ina mai godewa Allah da na kasance cikin mutanen da suka tsinci kan su cikin wannan wata, Allah kuma ya sa muna daga cikin bayin da za a ‘yanta. Ina kuma taya duk wani Musulmin duniya murnar zagayowar wannan wata mai alfarma, sannan kuma mu dage da addu’o’i don samun biyan bukatun mu na alkairi. Allah ya sa mu dace. Amin.

 

Ina mai godewa Allah da ya sake sada mu da wannan wata mai albarka. Zan kuma yi amfani da wannan dama domin kira ga ‘yan uwana musulmai da mu kara kaimi a yayin ibada don saboda mu kasance daga cikin bayin da Allah zai ‘yanta. Allah ya sa mu kammala azumi cikin koshin lafiya. Amin.

 

Ina mai godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya sa na kasance cikin musuan da suka sake tsintar kansu cikin wannan wata na Ramadan.

Ina kuma taya sauran ‘yan’uwa Musulmi murnar zagayowar wannan wata. Ina kuma kira ga al’ummar Musulmi da mu tashi tsaye wajen gudanar da ibadu tare da addu’o’in samun rahma da kuma neman zaman lafiya a kasar mu Nijeriya.

Allah kuma ya dafawa shugaban kasarmu.

 

Ina taya dukkanin Musulmin duniya murnar sake zagayowar watan Ramadan. Allah ya sa nu soma a sa’a mu kuma kammala cikin nasara. Allah ya sada mu da alkairin dake cikinsa, ma’ana Allah ya sa muna daga cikin bayin da za su rabauta a wannan wata.

Ina kira ga Musulmi baki daya da mu kara hobbasa a yayin ibada don ganin sun samu garabasar dake cikin wannan wata. Allah ya sa mu dace.

 

Tabbas duk Musulmi na kwarai idan ya tsinci kansa a irin wanann lokaci na watan Ramadan, ya kan yi farin ciki tare da mika godiyarsa ga Allah da ya sanya shi cikin jerin bayin da suka sake ganin wannan wata na Ramadan.

Haka kuma ina taya dukkanin musulman duniya murnar zagayowar wannan wata.

Ina kira ga jama’a da su yi amfani da wannan dama wajen yin addu’ar samun biyan bukatunsu. Allah ya sa mu gama lafiya.

 

Ina mai taya ‘yan’uwana Musulmai murnar zagayowar watan Ramadan. Allah ya sada mu da alkairan dake cikinsa.

Allah ya sa muna daga cikin bayin da za a ‘yanta. Sannan kuma ina kira ga ‘yan’uwana Musulmai da mu yawaita addu’a da ibadu a cikin wannan wata, domin wata mai alfarma wanda ake ‘yanta bayi a cikinsa.

 

Allah muna godiya gare ka sake nuna mana wannan lokaci. Ina rokonKa da sunayenKa tsarkaka da Ka sa muna daga cikin bayin da za a ‘yanta a wannan wata. Allah ka baiwa kasarmu zaman lafiya, Ka kuma karawa Shugaban Kasanmu Muhammad Buhari lafiya.  Allah ya sa mu kammala azumi lafiya, nagode. A sha ruwa lafiya.

 

Exit mobile version