Zargin Wuce Gona Da Iri: MOPPAN Za Ta Hukunta Bosho

Kungiyar ladabtar da jarumai maza da mata MOPPAN ta fitar da wata sanarwa a safiyar ranar talata cewa, za ta hukunta jarumin barkwanci nan Sulaiman Bosho bisa laifin wuce gona da iri a kan abinda darakta ya umarce shi.

A cewar Moppan: “Mun jima muna ganin kurakuran da Bosho yake yi a cikin fim, mun kiran shi don ya gyara amma ya kasa gyarawa.”

“Mun tuhumi daraktocin da suke da saka shi a cikin fim amma sun ce, su basu ga laifi ko munin kalamansa ba. Don hakane muka yanke hukuncin hukunta daraktocin da kuma shi jarumi Bosho.” In ji MOPPAN.

Majiyar Naija.com ta samu labarin cewa hukuncin da za ayi jarumi Bosho akwai tara wanda aka ci Bosho don wannan ya zama izna a gareshi dama daraktocin da suke bashi umarnin furta kalaman da ba su dace ba.

Da muka tambayi Bosho akan da wacce fuska ya kalli wannan hukunci? Sai ya amsa da cewa: “Wannan hukunci son ransu suka aikata, domin mutane sune ya kamata su gane laifin da muka aikata basu ba, domin mutane sune masu kallon mu, sune alkalai ba Moppan ba.”

 

Exit mobile version