Bikin Babbar Sallah: Gwamnatin Zamfara Ta Yi Wa Fursunoni 150 Afuwa

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya yi fursunoni 150 afuwa a babban kurkukun Gusau da ke tsaro mafi tsanani a jihar.
Babban Darakta, jami’an hulda da manema labarai na jihar, Yusuf Idris, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Gusau a ranar Asabar.
Bayanin da aka gabatar wa manema labarai ya bayyana cewa daga cikin wadanda aka yi wa afuwa sun hada da mutane biyar wadanda aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai.
Sauran wadanda aka yi wa afuwa sun hada da fursunoni biyar da aka manta da su, fursunoni 30 wadanda aka yanke wa hukunci, fursunoni 60 da ke jiran shari’a da kuma mata tara masu shayarwa.
Sauran sun hada da mutane 41 da aka ‘yantar saboda suna haddace Alkur’ani Mai Girma, da nakasassu, da tsofaffi da kuma wadanda suka kwashe sama da shekaru 20 ba tare ba tare da an yanke musu hukunci ba.
Sanarwar ta nakalto Matawalle yana shawartar wadanda aka yi wa afuwar da su yi dauki wannan ‘yancin da suka samu a matsayin wata dama ce daga Allah.
Gwamnan ya kuma bayar da gudummawar shan shanu biyar, buhunan shinkafa 100, raguna biyar, magunguna da sauran kayan abinci ga sauran fursunonin don murnar bikin babbar sallah.

Exit mobile version