Shi dai bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin ta kasa da kasa (CIIE) wani dandali ne inda kamfuna, kungiyoyi da kasashe ke taruwa su baje kolin irin kayan da suke da shi, ko kuma irin hidimomin da suke samarwa.
Kasar Sin, wadda ita ce kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, ta gudanar da bikin baje koli ta kasa da kasa (CIIE) a kan kayan da ake shigar da su kasar Sin tun daga ranar 5 ga wannan wata na Nuwamba har zuwa 10 ga watan a birnin Shanghai dake yankin gabashin kasar. Kimanin kasashe 17 ne daga Afirka suka samu halartar wannan gagarumin bikin tare da kafa rumfunansu domin baje kolinsu.
Nijeriya ba wai ta kasance daya daga cikin wadannan kasashe ba kadai, har ma an karrama ta da matsayin daya daga cikin manyan baki a wajen wannan taron baje koli.
Babu shakka ba abin mamaki ne ba kan irin wannan karramawa da ta samu, musamman idan muka yi la’akari da irin kyakkyawar alaka dake tsakanin kasashen biyu. Misali akwai alakar cinikayya kan amfanin gona kamar su Yazawa, Ridi da Cocoa, wadanda ake shigar da su kasar Sin. Irin wadannan amfanin gona suna daga cikin kolin da Najeriya ta baje a wajen wannan gagarumin taro. Baya ga amfanin gona, Nijeriya ta baje kolin al’adunta ta hanyar baje kolin tufafi da nau’ikan abincinta.
Wannan bikin baje koli ya kara jaddada aniyar kasar Sin ta bude kofarta ga kowa da kowa, musamman kasashen Afirka. Bugu da kari, Sin ta kuduri aniyar cire duk wani haraji kan kayayyakin da ake shigar da su Sin daga kasashen Afirka da suka kulla huldar diplomasiyya da ita, sabanin irin matakan rashin mutunci na rubanya harajin cinikayya da America ke yi kan kayayyakin da ake shigar da su kasar.
Babban abin lura a nan shi ne irin alfanun da Nijeriya za ta samu tare da sauran kasashen Afrika daga wannan bikin baje koli.
Na farko dai Nijeriya da sauran kasashen Afirka za su kara kaimi wajen noman irin waɗannan amfanin gona domin fitar da su zuwa Sin, hakan kuwa zai kara samar da aikin yi ga dubban ‘yan Nijeriya, abin da zai habaka kudaden shiga ga kasa.
Alfanu na biyu kuma shi ne fadada damar ingantawa da kara daga darajar irin wadannan amfanin gona da Nijeriya ke samarwa.
Sannan kuma akwai batun bunkasa dangantakar cinikayya tsakanin Sin da Nijeriya da ma sauran kasashen Afirka.
Sabo da haka wannan irin lamari na bude kofar cudanya tsakanin Sin da sauran kasashen duniya, musamman kasashe masu tasowa na Afirka, abin jinjinawa ga kasar Sin, kuma abin koyi ne ga sauran kasashen yammacin duniya. (Lawal Mamuda)














