Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Bikin Baje Kolin Canton Fair Karo Na 127 Ta Yanar Gizo Ya Nuna Manufar Sin Ta Kara Bude Kofa Ga Ketare

Published

on

Yayin bikin baje kolin hajojin da ake shigowa da su kasar Sin, da wadanda ake fitarwa daga kasar da aka fi sani da “Canton Fair” karo na 127 ta yanar gizo, kamfanonin kasar Sin da na kasashen ketare sama da dubu 26 sun yi nune-nunen kayayyaki ba rana ba dare a cikin kwanaki 10 da suka gabata, ‘yan kasuwa masu sayen kayayyaki dake kasashe da shiyyoyi da yawansu ya kai 217 sun yi rajista ta yanar gizo domin gudanar da cinikayya, an nuna hajoji sama da miliyan 1 da dubu 800 ta kafar bidiyo kai tsaye, an kammala bikin a ranar 24 ga wata cikin nasara.

Wannan shi ne karo na farko da aka shirya bikin ta yanar gizo, sakamakon barkewar annobar cutar COVID-19, lamarin da ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana nacewa kan manufar kara habaka bude kofa ga kasashen ketare, hakan ya kara shaida cewa, kasar Sin tana sauke nauyin dake wuyanta a matsayinta na kasar dake kan gaba a duniya a bangaren kiyaye tsarin samar da kayayyaki a fadin duniya.
Ana daukar bikin wanda shi ne gagarumin bikin cinikayyar kasa da kasa mafi girma kuma mafi tsawon tarihi a matsayin alamar cinikayyar waje ta kasar Sin, kana alamar bude kofa ga ketare ta kasar Sin. Yanzu haka ana fama da yaduwar cutar COVID-19 a sassan duniya, a don haka kasar Sin ta tsai da kuduri a farkon watan Afrilun da ya gabata cewa, za ta shirya bikin ta yanar gizo, hakan ba ma kawai zai biya bukatun ‘yan kasuwa masu sayen kayayyaki na kasashen ketare ba, har ma zai samar da damammaki ga kamfanonin ketare wadanda ke da niyyar shiga kasuwar kasar Sin.
Abun da ya fi jawo hankakin jama’a shi ne, yayin bikin nune-nunen kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin, kasashen da suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya sun karu, misali kamfanonin kasashen sun kai kaso 72 bisa dari, kana hajojin da suka samar sun kai kaso 83 bisa dari, lamarin da ya nuna cewa, shawarar ziri daya da hanya daya tana da babbar ma’ana wajen samun ci gaba yayin da ake fuskantar rikici, saboda suna nacewa kan manufar tattaunawa tare da ginawa da kuma cin gajiya tare.
Kasar Sin kasa ce mafi girma a fannin cinikayyar kayayyaki a duniya, idan tana gudanar da cinikayyar waje yadda ya kamata, lamarin zai taka rawa ga daidaiton tattalin arzikin duniya, yanzu an kammala bikin cikin nasara, ko shakka babu zai taimakawa daidaiton cinikayyar wajen kasar Sin da kyautatuwar tsarin samar da kayayyaki na kasa da kasa.
Bisa shirin da aka tsara, za a shirya bikin karo na 128 a karshen watan Oktoba mai zuwa, a sa’i daya kuma, za a gudanar da bikin CIIE karo na uku a watan Nuwamban bana a birnin Shanghai, wannan wata alama ce dake nuna yadda kasar Sin take yin kokari matuka domin ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: