Bikin Baje Kolin Cinikayyar Hidimomi Na Kasa Da Kasa Ya Shaida Fatan Kasar Sin Na Cimma Moriyar Bai Daya
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bikin Baje Kolin Cinikayyar Hidimomi Na Kasa Da Kasa Ya Shaida Fatan Kasar Sin Na Cimma Moriyar Bai Daya

byCMG Hausa
3 years ago
Kasar Sin

Yayin da ake ci gaba da gudanar da bikin baje kolin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa na shekarar 2022 ko CIFTIS a takaice, a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, masharhanta na ci gaba da bayyana fa’idojin wannan baje koli, da ma yadda yake kara haskaka manufar kasar Sin, ta ingiza cudanyar sassan kasa da kasa, da samar da ci gaba na bai daya ga dukkanin bil adama.

Fannin cinikayyar hidimomi na nufin saye ko sayar da hidimomi, wadanda ba su shafi kayan da ake sarrafawa ba, wato biyan kudi domin samun hidimomi kamar na sufuri, yawon bude ido, harkokin sadarwa, tallace-tallace, lissafi da aikin akanta, da musayar bayanai da dai sauran su.

  • Darajar Masana’antun Samar Da Kayayyakin Latironi Na Kasar Sin Na Karuwa Cikin Sauri

A bana, baje kolin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa na CIFTIS, wanda birnin Beijing ke karbar bakunci, ya hallara manyan baki 189 daga ciki da wajen kasar, baya ga kasashe da hukumomin kasa da kasa kimanin 71 da suke halartarsa. Babban burin kasar Sin na samar da wannan dandali dai shi ne kara bude kofa ga waje, da zurfafa hadin gwiwa domin ingiza kirkire-kirkire, wanda hakan wata muhimmiyar gudummawa ce ga ci gaban fannin ba da hidima na duniya baki daya.

A halin da ake ciki, wannan fanni na cinikayyar ba da hidima na kasar Sin na ci gaba da fadada, inda a watanni 6 na farkon shekarar bana, darajarsa ta kai kwatankwacin dalar Amurka biliyan 420. Kana kasar ta fitar da ayyukan ba da hidima da darajar su ta kai kudin Sin yuan tiriliyan 1.4.

A wannan gaba da kasar Sin ke gayyata sassan duniya su shiga a dama da su, a fannin bunkasa hada-hadar cinikayyar ba da hidima, sassan kasa da kasa na da wata dama mai kyau ta yin cudanya da koyi da juna, tare da nazarin fifikon da suke da shi a wannan muhimmin fanni.

A hannu guda kuma, Sin za ta ci gaba da yayata manufar bunkasa ci gaba mai inganci a fannin, da kara bude kofa ga sassan waje, matakin da zai tabbatar da nasarar burin da ake da shi, na wanzar da daidaiton ci gaban tattalin arziki da walwalar al’ummar duniya baki daya. (Saminu Hassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Za Mu Taimaka PDP Ta Fadi Zaben 2023 -Wike

Za Mu Taimaka PDP Ta Fadi Zaben 2023 -Wike

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version