Daga Haruna Akarada, Kano
Ranar Asabar din da ta gaba ta ne cibiyar kasuwanci ta Jihar Kano ta fara gudanar da bajekolin da ta saba yi duk shekara.
Wannan ne ya sa Wakilin LEADERSHIP A YAU ya samu ganawa da daya daga cikin shugabannin wannan Cibiya Alhaji Hassan Yaro, wanda shi ne Mataimakin Shugaban cibiyar na Jihar Kano.
Ya ce, an yi bikin bude wannan bajekolin na bana ne a ranar Asabar din da ta gabata 28 ga Nuwamba, 2020, inda Mataimakin Gwamnan jihar, Dr Nasiru Yausuf Gawuna, ya wakilci gwamna, shi ma Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya turo Hakimin Birnin Kano, don ya wakilce shi,
Yayin da ya ke bayani kan cigaban da a samu, ya ce, “an kara kwana uku, domin akwai kafe-kafe da mutane za su yi. Ka ga yanzu mu na da sauran sati biyu kenan.
“Wannan shekarar kusan a na yin wannan bajekoli a Legos da Abuja sakamakon zanga-zangar da ta faru wasu locacin ba su da nutsuwar yi kuma ba sa so shekarar ta wuce ba su yi ba, kuma yanzu haka akwai ’yan jihar Sakkwato da Zamfara tuni sun zo su na kafa rumfuna a wannan gurin.
“Muma mun dado tsari kamar yadda a ke yi a Dubai da komai na zamani mu ke yi kuma mun yi tsari na cigaba da zagayawa a cikin gari da mota, domin sanar da jama’a, sannan ga rediyo da jaridu duk su na bayar da gudunmawa ta hanyar labarai, kuma godiya da kokarin da a ke yi.”