Bikin Bazara Na Duniya Ne
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bikin Bazara Na Duniya Ne

byCGTN Hausa and Sulaiman
8 months ago
Bikin bazara

Yau Talata ita ce jajibirin bikin sabuwar shekarar kasar Sin, wato Bikin Bazara. A yau ne, daga Abuja zuwa birnin Beijing na Sin, Sinawa na haduwa tare da iyali, da gudanar da liyafa, da kallon shirin telabijin na kasaitaccen shagalin murnar bikin sabuwar shekara ta Sin. Sai dai ba Sinawa kadai ne suke murnar bikin ba. A birnin Paris na Faransa, da Sao Paulo na kasar Brazil, da dai sauransu, an mai da bikin bazara bikin da ake murnarsa. Kana a manyan biranen Afirka, kamar su Abuja da Lagos, bukukuwan murnar bikin bazara su kan janyo hankulan dubban mutane don su halarta. Sa’an nan, a karshen shekarar 2024, hukumar UNESCO mai kula da harkoki masu alaka da aikin ilimi, da kimiyya, da al’adu, ta sanya Bikin Bazara cikin jerin sunayen abubuwan gado na dan Adam, da ba na kayayyaki ba.

To, me ya sa bikin bazara samun karbuwa a duniya? A ganina, dalili shi ne, domin wannan bikin gargajiya ya kunshi dimbin abubuwa na bai daya da daukacin dan Adam suka yarda da su.

Na farko, bikin bazara ya nuna yadda dan Adam ke gadon al’adun gargajiya.

A Najeriya, akwai nau’in gangar da take iya “magana”. A da can, mutane sun yi amfani da gangar wajen samar da sakon murya. Kana a yanzu ta zama wani kayan kida mai salon musamman. To, tarihin gangar ya nuna yadda ake gadon al’adun gargajiya a tsakanin al’ummun Najeriya. Sa’an nan Bikin Bazara na kasar Sin shi ma kamar haka yake. Asalinsa shi ne bikin girmama kaka da kakani, da mazan jiya, sai dai zuwa yanzu bikin ya zama wani dandali mai kunshe da dimbin al’adu da fasahohi, duk da cewa yana ci gaba da dauke da sakonnin al’adu na rayuwar mutanen zamanin da, wadanda ke samun fahimta da karbuwa tsakanin al’ummun kasashe daban daban.

Na biyu shi ne, Bikin Bazara ya nuna tunanin dan Adam na kaunar iyali.

Kamar yadda ake samun haduwar iyalai sosai a lokacin bukukuwan kasar Najeriya, Bikin Bazara na Sin shi ma yana dora matukar muhimmanci kan haduwar mambobin iyali. A lokacin Bikin Bazara na Sin, mutane suna komawa gidajensu daga wurare daban daban, don halartar liyafar da a kan yi a jajibirin sabuwar shekarar Sin. Kana mambobin iyali za su yi hira sosai, da yi wa juna gaisuwa da fatan alheri, ta yadda za su karfafa kauna da zumunci a tsakaninsu.

Na uku shi ne, Bikin Bazara yana nuna halayyar dan Adam ta son zaman jituwa da kwanciyar hankali.

Ko da yake ana samun rikice-rikice da yawa a duniyarmu, amma ba za a rasa damar daidaita su ba, saboda cikin halayyar dan Adam akwai wasu abubuwan da za su tabbatar da zaman jituwa da ingantuwar harkoki. Mu dauki Bikin Bazara a matsayin misali: Wannan biki mai dadadden tarihi ya kunshi wani yanayi na zaman jituwa da murna, wanda ya sa mutane nuna girmamawa ga kaka da kakaninsu, da muhallin halittu, gami da kaunar iyali, da abokai, yayin da suke haduwa da juna, da musayar gaisuwa da fatan alheri a tsakaninsu. Wadannan abubuwa sun karfafa hadin kan iyali, da unguwa, gami da na al’umma, tare da shaida yadda dan Adam ke son abokantaka da zaman lafiya.

Bikin Bazara na kasar Sin, biki ne na duniya. Saboda ta wannan biki, muna iya ganin wasu bangarorin bai daya na halayyar dan Adam: Wato dukkanmu na bukatar kaunar ‘yan uwa, da son kyakkyawan muhallin rayuwa. Kana dukkanmu muna kokarin gadon al’adunmu na gargajiya, wadanda suke da asali masu kama da juna. Wadannan abubuwa na bai daya tushe ne ga yunkurinmu na kawar da sabanin ra’ayi, da gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya.

Yadda Bikin Bazara ke samun karbuwa a duniya ya sa mun samu wata kyakkyawar fata na son ganin a nan gaba, mutanen kasashe daban daban sun kara hadin kai da juna, da tabbatar da karin yanayi na jituwa, da kwanciyar hankali, da ci gaba, a duniyarmu. (Bello Wang)

 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka
Ra'ayi Riga

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Labaran Xinjiang A Zane: Manyan Sauye-Sauye A Fannin Ba Da Ilmi A Xinjiang
Ra'ayi Riga

Labaran Xinjiang A Zane: Manyan Sauye-Sauye A Fannin Ba Da Ilmi A Xinjiang

September 30, 2025
Alfanun Harshen Mandarin A Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Alfanun Harshen Mandarin A Kasashen Afirka

September 29, 2025
Next Post
Da Ɗumi-ɗumi: Wata Tankar Mai Ta Sake Fashewa A Neja

Da Ɗumi-ɗumi: Wata Tankar Mai Ta Sake Fashewa A Neja

LABARAI MASU NASABA

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version