Bikin Bazara Na Kasar Sin Ya Zo Da Salo Na Musamman A Bana

Daga Saminu Hassan

Kamar dai yadda kasashen duniya daban daban ke gudanar da manyan bukukuwa ko dai na addini ko al’ada, irin su bikin kirsimeti ga mabiya addinin kiristanci, ko bikin sallah na al’ummar musulmi, ko bikin girbi da wasu al’ummu dake sana’ar noma a sassan duniya daban daban ke yi, domin murnar kewayowar wani lokaci na musamman, a nan kasar Sin, biki mafi girma da kayatarwa shi ne bikin Bazara ko bikin samuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar.

An kayata wurare daban daban domin alamta zuwan bikin Bazara a kasar Sin.

Ko da yake, bisa sauye-sauyen zamani, ayyukan da ake yi a lokacin bikin na bazara suna kara sauyawa, a hannu guda ana iya cewa, hanyoyin da al’ummar Sinawa ke bi don gudanar da shagulgulan bikin suna da tsuhe daya. Kaza lika matsayin bikin bazara a zamantakewar Sinawa ba zai taba sauyawa ba, musamman ta fuskar kima da darajar sa.
Bisa tarihi, bikin bazara na kasar Sin, yana da tarihin sama da shekaru 4000. Duk da cewa da can, ba a kiransa da bikin bazara, kuma ba shi da takaimaiman lokaci, zuwa shekara ta 2000 da wani abu kafin haifuwar Annabi Isa Alaihissalam, Sinawa na daukar tsawon lokacin juyawar tauraron da ake kira “Jupiter” sau daya, ta zama “Sui” daya, kuma akan kira bikin bazara da sunan “Sui”.

An yi nune-nunen wasannin bikin Bazara a Wellington na New Zealand.

Kaza lika, kafin shekara ta 1000 gabanin haifuwar annabi Isa Alaihissalam, mutane na kiran bikin bazara da sunan “Nian”. A wancan lokaci, kalmar “Nian” tana da ma’anar samun amfanin gona mai armashi, wato idan an samu amfanin gona mai armashi, sai a ce “akwai babban Nian”.
Bisa al’adar jama’ar kasar Sin, bikin bazara na farawa ne tun daga ranar 23 ga watan Disamba na kalandar gargajiya ta kasar, kuma ana ci gaba da shagulgulansa har zuwa bikin Yuanxiao, wanda ake yi a ranar 15 ga watan farko na sabuwar shekara, ke nan tsawon bikin na kaiwa wajen makwanni 3.
A tsakanin wannan lokaci, kwana daya da yini daya, wato jajiberin sabuwar shekara, ranar 30 ga watan Disamba da dare, da ranar 1 ga watan farkon shekara su ne suka fi muhimmanci da kasaita. Ana iya cewa, su ne ma lokacin da bikin ya fi tashe. Domin yin maraba da bikin bazara, daga birane zuwa kauyuka, mutane suna gudanar da ayyuka daban-daban na shirin bikin.

Ana aiwatar da matakan kandagarki yayin bikin bazara.

A kauyuka, tun daga watan Disamba na kalandar kasar Sin, a kan fara ayyukan share fagen zuwan bikin. Iyalai manoma da yawa sukan share daki, su wanke tufafi, da barguna, da kauda rubabbun abubuwa, ta yadda za a samu sabon yanayi na jin dadin zaman rayuwa. Daga nan sai iyalai su shiga sayen kayayyaki iri-iri daga kasuwa domin bikin bazara, kamar alewa, da kayan zaki, da nama da ‘ya’yan itatuwa, ta yadda za su samu isashen abinci domin kansu, da kuma karbar baki a lokacin bikin.
A manyan birane kuma, ana fara ayyukan share fage zuwan wannan kasaitaccen biki ne tun da dadewa. Sassan masu nuna fasahohin al’adu, da kungiyoyin masu nuna bajimta, suna shirya wasanni daban daban masu ban sha’awa. Su ma gidajen rediyo da na talabijin, sukan yi shirye-shirye iri daban-daban na musamman. Ban da wannan kuma, akan shirya baje-koli cikin manyan lambunan shan iska daban- daban, ta yadda mutane masu yawon shakatawa, za su samu damar yin shagulgula masu nishadantarwa.

Wasu mazauna Beijing na gwada fasahar zanen gargajiya a lokacin bikin bazara.

Manyan kantuna kuwa, sukan yi odar hajoji daga wurare daban- daban, na cikin kasa har ma da na kasashen waje, domin biyan bukatun ‘yan birni a lokacin bikin na bazara. Sinawa kan kashe makudan kudade wajen sayen kayayyaki a lokacin bikin bazara.
A lokacin wannan muhimmin biki, Sinawa na son cin abinci mai kunshe da nama, da ganyaye nau’oi daban daban. Daga cikinsu tilas ne a samu “Tofu” da akan yi daga waken soya, da kuma “Yu” wato kifi, saboda sunan sa da kalmar “Fuyu” wadda lafazinta cikin Sinanci ya yi daidai da na kalmar “arziki”. Hakan dai tamkar fatan Alheri ne!
A arewancin kasar kuwa, yawancin iyalai sukan ci abincin da ake kira da “Jiaozi” a jabibirin bikin da dare, wato iyalai sukan yi “Jiaozi” tare, wanda abinci ne da ake yi ta hanyar kunsa nama da aka nika, cikin garin alkama mai da’ira, sai a dafa cikin tafasasshen ruwa, bayan ya dahu, sai a rika cin “Jiaozi” da kayan yaji. A lokacin, iyalin gida guda za su kewaye tebur daya suna cin “Jiaozi” tare cikin halin annashuwa.
A jajiberin bikin da dare, mutane sukan ki yin barci, suna ta wasanni iri-iri cikin murna da fara’a duk tsawon dare. Ana yin hakan ne domin alamta wucewar tsohuwar shekara, da shiga cikin sabuwar shekara. A da, a lokacin zuwan sabuwar shekara, mutane sukan harba wutar gimbiya ko knockout da turanci, domin murnar bikin. Ana yin wannan al’ada ce domin korar miyagun shaidanu. Sai dai a baya bayan nan, an yi matukar rage yin hakan, saboda kaucewa hadurra, da kiyaye muhalli.
A ranar daya ga watan sabuwar shekarar, a kan yi ado da kaya masu kyau, ana ziyartar juna, tare da yiwa ‘yan uwa da abokan arziki murnar zuwan sabuwar shekara. Bayan komawa gida kuma, sai a ci gaba da shan alewa, da ‘ya’yan itatuwa, kuma ana shan shayi tare da hira. Idan an yi sabani cikin shekarar da ta wuce a tsakanin dangi da aminai, sai a yi amfani da wannan lokaci wajen yiwa juna fatan alheri a wannan lokaci, daga nan an riga an samar da fahimtar juna ke nan.
Bugu da kari, akan yi rubutun wakoki na fatan alheri, a jera fitilu masu launi daban daban musamman ma launin ja, domin murnar wannan biki. Har ila yau, a lokacin bikin, kasuwanni sukan sayar da zane-zane na sabuwar shekara, da takardun waka kwar biyu iri daban-daban, wadanda ke bayyana zaman jin dadin jama’a, da ayyukan da suke yi cikin fara’a.
Kalandar gargajiya ta Sinawa na kunshe da dabbobi 12, kuma duk dabba daya na alamta shekara guda. A bana an shiga shekarar Sa, akwai kuma shekarun da kan zo kamar na Bera, da Doki, da Maciji, da Alade da dai sauran su.
Shin ko me ya banbanta bikin na bana da sauran wadanda suka gabace shi?
Da zarar an ambaci shekarar 2020 da ta gabata, abun da kan yi saurin fadowa zukatan al’umma shi ne bullar cutar numfashi ta COVID-19, wadda a bara, ta fado lokacin da ake tsaka da bikin bazara na Sinawa. Ko shakka ba bu, bullar wannan cuta a lokacin ta ragewa Sinawa armashin bikin na bara, domin a lokacin ne mahukuntan kasar Sin suka shiga kokarin daukar matakan dakile bazuwar cutar ta hanyoyi daban daban, ciki har da killace wasu birane da takaita zirga zirgar al’umma a wasu sassa.
Bayan shawo kan bazuwar cutar a kasar Sin, a bana ana iya cewa kasar Sin ta san inda ta dosa, game da yaki da annobar, domin kuwa tuni har an samar da nau’oin alluran rigakafin COVID-19 daban daban kirar kasar ta Sin. An kuma fara yiwa rukunoni mafiya fuskantar yiwuwar harbuwa da cutar rigakafin.
Amma fa duk da haka, ana iya cewa, yaki da cutar COVID-19 ba aiki ne na rana guda ba. Kamar yadda hukumar lafiya ta duniya WHO ta sha bayyanawa, aiki ne da zai dauki duniya tsawon lokaci kafin kaiwa ga cikakkiyar nasarar sa. Fahimtar hakan ne ma ya sanya mahukuntan Sin, suke ci gaba da daukar karin matakan kandagarkin bazuwar cutar ba tare da yin sassauci ba.
A bana, a lokacin bikin na bazara da ya fado cikin mako na biyu na watan Fabarairun nan, Sinawa da dama sun zabin yin hakuri da tafiye tafiye na komawa garuruwansu, wanda hakan ya sa bisa kiyasi, yawan fasinjojin dake tafiye-tafiye yayin bikin bazarar, a bana suka ragu da kaso sama da 60 cikin dari, idan aka kwatanta da na shekarar 2019. Kaza lika wani rahoton binciken da aka yi ya nuna cewa, yan kwadago manoma fiye da kaso 77 cikin dari, sun zabi yin murnar sabuwar shekara a wuraren da suke aiki.
Sauyi daga tafiye-tafiye zuwa gudanar da murnar bikin a wurin aiki, a bana an ga sauyin hanyar murnar bikin bazara ta alummun kasar Sin, lamarin shi ma ya nuna ingancin tsarin tafiyar da harkokin kasa na kasar Sin.
Me mahukunta ke cewa game da hakan?
A gabannin bikin bazara, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci lardin Guizhou domin rangadin aiki, inda ya shiga wata kasuwa dake lardin, domin kara fahimtar hakikanin yanayin da alummun kasar ke ciki, ta yadda za a tabbatar da samar da isassun kayayyakin da ake bukata da farashin da ya dace, yayin murnar bikin na bazara.
Shugaban ya ce, domin tabbatar da biyan bukatun al’ummun da suke murnar bikin sabuwar shekara a wuraren da suke aiki, gwamnatin kasar Sin ta fitar da wasu manufofi. Alal misali a birnin Beijing fadar mulkin kasar, gwamnatin birnin ta bude lambunan shan iska ga masu yawon shakatawa kyauta, kuma ta samar da takardun sayayya ta yanar gizo, da takardun wasan kankara kyauta ga mazauna birnin. Kana ta shirya wasannin nishadantarwa iri daban daban yayin bikin na bazara.
A lardunan Zhejiang da Guangdong kuwa, gwamnatocin lardunan sun samar wa yan kwadagon da suke lardunan daga sauran larduna kudin rangwame, da kudin sayen damar amfani da yanar gizo ta wayar salula da sauransu.
Masharhanta da dama na ganin cewa, bayan da kasar Sin ta kai ga jure kalubale da yaduwar cutar COVID-19 ta haifar mata, ta bayyana a fili cewa, tsarin tafiyar da harkokin kasa na kasar Sin ya kyautata, kuma har kullum gwamnatin kasar tana daukar matakan da suka dace, yayin da take kokarin kandagarkin annobar, kuma karfin gudanar da harkokin kasa na kasar Sin ya karu, matakan da suka yi matukar burge alummomin kasa da kasa.
Wata muhimmiyar gaba da ta karawa bikin sabuwar shekarar Sinawa na bana armashi ita ce, karuwar yawan masu amfani da fasahar 5G domin shiga kafofin yanar gizo. Karkashin hakan, Sinawa da dama sun tattauna da iyalan su dake nesa da su, wasu sun yi sayayya, ko ziyartar gidajen adana kayan tarihi ta kafofin yanar gizo. Masharhanta na ganin fadadar fasahar 5G mai ba da damar amfani da yanar gizo cikin sauri, ta taimakawa Sinawan wajen gudanar da wannan muhimmin biki cikin matukar jin dadi.
Alkaluma sun nuna cewa, daga ranar 4 zuwa 11 ga watan Fabarairun nan, lokacin da ake tsaka da bikin bazara, a manhajar Tiktok da ake amfani da ita wajen dora gajerun bidiyo, an kalli sakwannin gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta Sinawa sama da sau biliyan 50.6.
Tun bayan samar da lasisin fara kafa tashoshin internet na 5G a kasar Sin a watan Yunin shekarar 2019, kawo karshen shekarar bara, an kafa sama da tashoshin 5G 700,000, da kuma kananan tashoshin hada fasahar ta 5G sama da miliyan 200.
Murnar bikin bazara a wuraren aiki alama ce ta nuna halin kishin kasa na Sinawa
Bahaushe kan ce “Himma ba ta ga rago”, domin kuwa tun bayan barkewar annobar COVID-19, alummun kasar Sin da yawansu ya kai biliyan 1.4 suka hada kai karkashin jagorancin gwamnatin kasar domin ganin bayan wannan annoba, kuma kokarinsu wanda ya burge alummun kasa da kasa ya kai ga samun sakamako mai gamsarwa.
Yanzu haka kuma, alummun kasar Sin sun sake nuna wa duniya halin kishin kasarsu, ta hanyar daukar matakai, ciki har da murnar bikin bazara a wuraren da suke aiki, da haduwa ta yanar gizo da sauransu, kamar yadda babban mai ba da shawara ga babban jamiin hukumar lafiya ta duniya Bruce Aylward ya bayyana, cewa ko wane Basine na sauke nauyin dake wuyansa yayin da ake kandagarkin annobar COVID-19.
Bana shekarar saniya ce, bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, kuma bisa aladar Sinawa, saniya na alamta kwazo da karfi, wadanda kuma Sinawa suka nuna su a zahiri, yayin da suke murnar bikin bazara na wannan shekara. Duk da cewa, Sinawa da yawan gaske sun yi murnar bikin a wuraren da suke aiki, amma zukatansu a hade suke, kuma ko shakka babu, kokarinsu zai ciyar da kasar Sin gaba yadda ya kamata.

Exit mobile version