Bikin Cika Shekara 6: Ganduje Ya Baje Kolin Nasarorin Gwamnatinsa

Gwamnatinsa

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

A wani bangare na bukukuwan cika shekara shida a kan karagar Mulki, Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi bayani dalla-dalla kan nasarorin da aka samu a bangarorin ma’aikatun gwamnati daban-daban.

Inda ya ba da tabbacin ci gaba kamar yadda ya fara tun farkon hawan sa mulki a ranar 29 ga watan mayun Shekara ta 2015. Kamar yadda babban Daraktan yada labarunsa Abba Anwar ya shaida wa LEADERSHIP A Yau.

Lokaci ba zai ba da damar jero dukkan nasarorin da aka samu ma’aikatun ba, Wanda hakan tasa dole an takaita a ma’aikatun biyar kacal na Jihar Kano.

Taron da ya gudana a babban dakin taro na Koronashen dake fadar Gwamnatin Jihar Kano ya samu halartar kakakin Majalisar dokokin Jihar Kano tare da sauran ‘yan Majalisu, ‘yan Majalisar wakilai dana dattijai na kasa, Sarakuna, Shugabannin Kananan Hukumomi, kungiyoyin dalibai da sauranau.

Kwamishinonin da suka gabatar da jawaban nasarorin da aka samu a ma’aikatun su sune na, ilimi, Lafiya, Kananan Hukumomi da Masarautu da Kuma Ma’aikatar ayyuka cigaban aikace aikace da muhalli.

Bayan kammala jawabansu daban daban sai Gwamnan ya kammala da abinda ya kira cikakken takaitaccen jerin nasarorin da Gwamnatin sa ta samu, yace, “Nawa shi ne bayar da bayani a takaicen takaitawa kamar yadda ku kaji daga ma’aikatun mu,”

“A bangaren Ilimi,  abinda muka fahimta shi ne gudunmawa da jajircewar da muka nuna, hakan tasa muka sa wannan bangare a sahun gaba. Misali tun kafin shirin mu na ilimi kyauta kuma wajibi ga kowa tun daga matakin firamare har zuwa sakandire, Gwamnatinmu nayin duk mai yiwuwa domin bayar da namu kason a bangaren batun Ilimi bai daya (UBEC) tun daga shekara ta 2015 zuwa yau.

Muna fitar da Naira Biliyon 1.5 duk shekara a matsayin kason tallafinmu ga bangaren ilimin bai daya na kasa, wanda jimla muke biyan Naira Biliyon 3 duk  shekara. Muna biyan duk abubuwan da ake bukata ba tare da wani jinkiri ba domin ci gaba da gudanar da harkokin ilimin kyauta kuma wajibi ya sa muka samu nasarar da ake bukata.” Inji Gwamna Ganduje.

Batun samar da  asusun tallafin ilimi, Gwamnan ya bayyana cewa, hakan ya taimaka kwarai da gaske wajen Inganta sashin ilimin da kulawa ta musamman.

“Karkashin asusun Tallafin, kaso biyar ake cirewa daga cikin kason harajin mu na cikin gida (IGR), kaso daya daga kason Kananan Hukumomin Jihar Kano da Kuma kaso biyu na dukkanin kwangilolin da aka bayar,” Inji Shi.

A bangaren shigar da makarantun almajirai cikin tsarin Ilimi kyauta Kuma wajibi, Gwamnatin Jihar Kano a cewar Gwamnan ta gina makarantu almajirai 3 manya a Jihar Kano.

A bangaren Lafiya, yace, Gwamnatinsa ta kirkiro asusun hadin guiwa na harkar Lafiya, da asusun amintattun na harkar Lafiya, daga darajar asibitoci a shelkwatar sabbin Masarautu hudu masu gadaje 400-400 kowannensu.

Ya kara da cewa,” baya ga wadannan manyan nasarorin da aka cimma,  mun kuma gina sabuwar cibiyar lura lalurar da cutar kansa irinta zamani wacce ake fatan kammala aikinta a watan disambar shekarar da muke ciki. Haka kuma  mun samu nasarar yakin da ake da annobar Kirona.

Amma hakan baya nufin mu mike kafa kan kokarin da muke. Zuwa yanzu mun horar da sama da ma’aikatan sa kai 1,000 da suke taimakawa wajen lura da matakan kariya ga annobar Korona.”

“A Kananan Hukumomin mu na Jihar Kano,  wannan Gwamnati ta bada kulawa ta musamman kan ayyuakan hadin guiwa. Mun raba tallafin dubban daruruwan matasa a fadin Kananan Hukumomin Jihar Kano 44,” Inji shi

Gwamna Ganduje ya jinjinawa yadda aka samu ingantaccen zaman lafiya a Jihar Kano tun zuwanmu ofis, ya kara da cewa,  “Jihar Kano ce tafi kowacce jiha a kasarnan zaman Lafiya.  Zamu kara himmatuwa wajen dorewa akan haka. A wannan gaba nake godewa Jami’an tsaro bisa kyakkyawan aikin da suke a wannan bangare.”

“Ba Zan manta da ma’aikatanmu a Jihar Kano ba,  wanda idan ba tare dasu ba, da abubuwa da yawa ba’a samu nasarar suba. Muna  mutukar godiya ga wadannan ma’aikata. Mun kuma aminta kwarai da gaske da cewa,  idan wasu batutuwa suka taso tsakaninmu dasu, mun hakikance Tattaunawar da kyakkawar fahimta da yin aiki tare a tsakaninmu. Muna biyan albashi aduk wata ba tare da jinkiri ba,” Inji shi.

Da yake gabatar da jawabinsa alokacin taron, kakakin Majalisar dokokin Jihar Kano Alhaji Hamisu Ibrahim Chidari cewa ya yi,  a cikin wadannan so gohekarun 6 na wannan Majalisar dokoki, ” mun Amince da da samar  da kudirce-kudurce 100 a tsawon shekarun da suka gabatar, sannan mun zartar da dokoki sama da 60 wadanda yanzu sun zama doka.”

Ya jero wasu daga ciki akwai irinsu dokar zuba hannun jari ta shekara ta 2015 (1436 AH), dokar  hadaka ta harkar Lafiya ta shekara 2016 (1437), dokar asusun Tallafin harkar Lafiya ta shekara ta 2017 (1438),  dokar  sabbin asibitoci irin na zamani ta shekara 2018 (1428), da gyaran dokar  masarautu.

Exit mobile version