Bikin Dimokuradiyya: Gwamnan Adamawa Ya Yi Afuwa Ga Fursunoni 9  

Afuwa

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamnan Jihar Adamawa, Alhaji Ahmadu Fintiri, ya yanke shawarar yin yafiya da afuwa ga fursunoni tara a cikin bukuwan ranar dimukuradiyya da aka gudanar a jihar na wannan shekarar.

Gwamnan sai ya jinjina wa al’umman jihar a bisa jajircewa wajen ganin mulkin demokradiyya ta samu inganci a karkashin gwamnatinsa da ma na gwamnatocin baya, yana mai misalta hakan a matsayin cigaba mai ma’ana.

“Za mu cigaba da tabbatar da alkawuran da muka yi sun samu aiwatuwa, za mu tabbatar mun cika su, gwamnati za ta ci gaba da jawo kowa a jika wajen tafiyar da harkokinta, tare da baiwa kowa damarsa da kimarsa, sauke nauyin da ke kanmu da kuma tabbatar da aiwatar da ababen da zasu inganta rayuwar al’umma tare da kare musu rayukansu da dukiyarsu duk da matsatsin tattalin arziki da ake fama da shi a irin wannan lokacin.”

A sanarwar manema labarai da babban sakataren yada labaran gwamnan jihar, Malam Mumwashi Wonosikou ya fitar, gwamnan ya nuna tsarin demokradiyya a matsayin hanya mafi daewa na shawo kan matsalolin da suke akwai a wannan lokaci.

Ya ce, manufarsu ita ce cigaba da yin mulkin demokradiyya wajen tabbatar da samar da ayyukan raya jihar da kyautata walwala da jin dadin kowa, ya nemi jama’a da su cigaba da baiwa demokradiyya cikakken dama domin ingantuwar rayuwa a kowani lokaci tare da fatan kai jihar Adamawa zuwa mataki na gaba.

Exit mobile version