Connect with us

LABARAI

Bikin Gadir Na Bana A Lakwaja: An Sake Jaddada Muhimmancin Hadin Kan Musulmi

Published

on

An bayyana ranan bikin Idin Gadir a matsayin rana mai muhimmanci a tarihin addinin musulunci. Wani malamin addinin musulunci daga kasar Iran, Malam Ibrahim Yaro Iran ne ya bayyana hakan a kasidar daya gabatar a wajen bikin na Gadir da kungiyar mazhabar shi’a, wato Ahlul Bait ta shirya a birnin lakwaja na Jihar Kogi a jiya asabar.

Kungiyar ta Ahlul Bait ta shirya bikin ne don tunawa da shekarar da Annabin tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi hudubarsa ta karshe inda kuma a wannan lokaci ya zabi Imam Ali (RA) a matsayin Halifansa a garin Gadin dake kusa da birnin Makka. Da yake jawabi a wajen bikin na Gadir, Mallam Ibrahim Yaro Iran yace lamari na halifanci, abu ne mai girma wajen Allah ,inda ya kara da cewa Allah (SWT) ne ke da iko da kuma hukuncin zabar wanda yaga dama amma kuma cikin ikonsa Ya baiwa Annabi Muhammadu umurnin zabar wanda zai gaje shi bayan ya bar duniya. Malam Yaro Iran kazalika ya yi bayanin cewa Allah cikin basirarsa da hikimarsa ya zabi kaninsa, wato sayyidina Ali RA) saboda nagartarsa da jaruntakarsa da iliminsa da kuma tsoron Allah da yake dasu.

Malamin addinin musuluncin wanda har ila yau ya yi magana game da irin kalubalen da Annabin tsira ya fuskanta wajen zabar halifansa, ya yi bayanin cewa shugabanci abu ne mai girma, lamarin dake bukatar mutum adali, kamili, mai gaskiya da kuma mai ingataccen ilimi don tafiyar da jagoranci na gari .Malam yaro Iran ya kuma yi kira ga al, ummar musulmi dasu ji tsoron Allah tare da bauta masa kamar za su koma garesa a yau. Har ila yau ya shawarci musulmi dasu dage wajen neman ilimin zamani da muhammadiya don bada gudunmawar su wajen ci gaban addinin musulunci da kuma samun tsira a nan duniya da kuma can lahira.

Shima a tasa laccar daya gabatar, Malam Rabiu Basambo Iran wanda ke zaune a karar ta Iran ya ce, duk da cewa a damukuradyiya ta ba jama, a damar wadanda za su wakilicesu ,amma kuma a cewar sa, ainihin wadanda jama, a ke zabar, su suke danne su.  Don haka ne ya yi kira ga musulmi dasu zabi shugabanni nagari wadanda za su fitar masu da kitse a wuta .Har ila yau yayi kira ga gwamnatin tarayyar Nijeriya data gaggauta sako jagoran mazhabar Shi’a,Sheikh Ibrahim El-zakzakky da Uwargidansa harma da sauran mabiyansa duk da kotu ta bada umurnin sake sa. Ya ce, tauye hakkin dan Adam ne gwamnati ta ci gaba da tsare shaihun malamin.

Shugaban bikin kuma mamba mai wakiltar mababar lakwaja ta daya a majalisar dokokin jihar Kogi, Hon. Umar Ahmed Imam kira ya yi ga musulmi dasu yi aiki da koyarwar Kur’ani ani da Hadisi don ciyar da musulunci gaba, inda har ma ya maimaita bukatar akwai wajen ganin musulmi sun hada kawunansu idan aka yi la, akari da irin halin da kasar nan ke ciki. Daga nan ya taya musulmi murnan kammala Hajjin bana cikin nasara.

Tunda farko a jawabinsa,Jagoran kungiyar Ahlul Bait dake Lakwaja, Malam Suleiman Arrada kira ya yi ga mambobin kungiyar dasu hada kawunansu tare da inganta manufofin kungiyar, inda kuma ya kara da cewa kungiyar ta shirya taron laccar ne domin tunatar da al’ ummar musulmi hudubar manzon Allah ta karshe da ya yi wa mabiyansa kafin ya bar duniya .Ya kuma bukaci mambobin kungiyar da suyi aiki da ka’idoji  da kuma dokokin addinin musulunci wajen zabar shugabanni,  sannan a karshe yayi kira ga shugabannin dasu rika gudanar da adalci ga mabiyansu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: