Daga Bello Hamza,
A daidai lokacin da ake fuskantar matsalolin tsaro a fadin tarayyar kasar nan, kungiyar kiristocin Nijeriya ta CAN ta bukaci kirsitocin Nijeriya su rungumi akidar zaman lafiya da juna tare da kuma tabbatar da taimakon al’umma don kuwa hakan na daga cikin sirrorin da ke tattare da bukukuwan Ista.
kungiyar ta bayyana haka ne a takardar sanarwar da shugabanta, Rabaren Reb Samson Ayokunle, ya sanyawa hannu aka kuma raba wa manema labarai a Abuja ranar Juma’a, ya kuma ce,wannan lokaci ne da kiristoci za su fuskanci addu’o’i don fita daga cikin matsalolin tsaro da ake fuskanta a kasar nan.
Ya taya Kiristocin murnar bikin na Ista ya kuma nuna jin dadinsa da kasar bata cikin kulle a wannan karon kamar yadda aka yi irin wannan bikin a shekarar da ta gabata saboda annobar cutar Korona da aka fuskanta.
kungiyar ta kuma ce, “Yadda aka kawar da dutse daga kabari ne, ta haka muke fatan kawar da dukkan matsalolin da ke fuskantar kasar nan kamar, hare-haren ‘yan ta’adda, garkuwa da jama’a hare-haren makiyaya, kisan tsarface-tsaface da fashi da makami da kuma rashin aikin yi ga dinbin matasanmu da kuma dukkan sauran matsalolin da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu da sunan Yesu Almasihu.”
kungiyar ta kuma bukaci al’ummar Kirsita na kasar nan su cigaba da gudanar da addu’o’i don kuwa Alllah na tare da masu addu’a.