Daga Rabi’u Ali Indabawa, Abuja
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya taya ɗaukacin Al’ummar Kiristan duniya, musamman ma na Nijeriya murnar bikin Ista; bikin dai yana alamta tunawa da zagayowar ranar da Almasihu ya farfaɗo ne.
A saƙon nasa, Dr. Saraki ya hori Kiristoci da su kwaikwayi ɗabi’ar sadaukarwa don hakan zai haifar da bunƙasa da ɗorewar Nijeriya.
Dr. Saraki ya bayyana hakan ne a wata sanarwar manema labarai da ofishin yaɗa labaransa ya fitar yau a Babban Birnin Tarayya, Abuja. Ya ce, bikin Ista na alamta sadaukarwar da Yesu Almasihu ya yi domin amfanuwar al’umma, kuma duk wanda ke biyayya da ɗa’a ga koyarwarsa dole ne ya yi koyi da halayensa nagartattu domin amfanin kasarsa da ma duniya baki-ɗaya.
Ya ƙara da cewa, a wannan lokaci da Nijeriya ke fuskantar matsalolin da suka shafi harkar tsaro, tattalin arziki da sauransu, dole ne ‘yan ƙasa su kasance na gari su kuma yi koyi da halayen kwarai na Almasihu don a samu a fice daga wannan halin da ake ciki.
“Ina kira ga ‘yan Nijeriya da su yi koyi da ɗabi’ar ƙaunar juna da kuma ƙaunar ƙasasarsu. Ina da tabbacin cewa idan muka yi hakan zai taimaka mana wurin magance matsalolin da ke neman tarwatsa mana ƙasa, kuma za a samu haɗin kai.
“Dole ne mu yi amfani da wannan dama wurin bayyana cewa dukkaninmu ‘yan Nijeriya ne kafin kasantuwarmu Kirista ko Musulmi. Duk ‘yan Nijeriya, ba tare da la’akari da abin da suke bauta wa ba, dole mu kasance masu tsoron Allah ba kawai mu riƙa amsa sunan masu addini ba.
“Ina ƙara taya ‘yan uwanmu Kirista murnar bikin ranar Ista ta shekarar 2021.” Inji Saraki