Abubakar Abba" />

Bikin Mako Na Mabiya Mabambanta Addiinai: Mata Musulmai Sun Rabar Da Kyaututtuka Ga Coci-Coci A Kaduna

Don gudanar da shagulgulan mako na mabiya mabambanta addinai a jihar Kaduna, Jakadar wanzar da zaman lafiya Hajiya Hajiya Ramatu ta kai ziyara ga Coci-Coci da ke cikin jihar Kaduna tare da rabar masu da kyaututtuka don wanzar da zaman lafiya da kara kaunar juna.
A jawabin ta a lokacin bayar da gundummowar Hajiya Ramatu ta ce, Majalisar dinkin duniya ce ta ware ranar don daukaka zaman lafiya a daukacin fadin duniya gaba daya.
Ramatu ta yi nuni da cewar, hada a tsakanin mabiya mabambanta addinan biyu an samu nasara wajen wanzar da zaman lafiya, musammana jihar Kaduna. Ta kara da cewar, anyi hakan ne don tabbatar da yafiya a tsakanin mabiya mabanbanta addinan biyu da ke jihar, musamman don a kawar da daukacin rikicin addini da na siyasa da ke addabar kasar nan. Ramatu ta yi kira ga mabiya mabambanta addinai su fi mayar da hankali wajen ilimantar da ‘ya’yansu da kuma koya masu girmama addinin kowa don kara wanzar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin juna.
Ta ce, Litattafan masu tsarki Alkur’ani da Bayibil sun horas da mabiya a kan mahimmancin zaman lafiya. Ta sanar da cewar, a shekaru biyu da suka shige, ta rabar da Bayibil guda 50 da aka fassara su da harshen Hausa don wanzar da zaman lafiya. Ta jaddada mahimmanci kakkafa cibiyoyin gudanar da nazarin wanzar da zaman lafiya. Da yake karbar kyaututtukan a madadin ma’aikatan coci-cocin da suka amfana, Fasto Yohanna Buru ya nuna jin dadinsa, inda ya yi kira ga mabiya addinan biyu su ci gaba da zaman lafiya da junansu. Ya ce, a kwanan baya su ma kiristoci sun rabar da tabarmi da Butoci ga wasu masallatai da ke cikin jihar da kuma yi masu fenti don kara wanzar da zaman lafiya. Makon na mabiya mabambanta addininan, ana gudanar da shi ne a dukkan farkon makon watan Fabirairun ko wace shekara.

Mata Ne jigon Tattalin Arzikin Kasa
A hirar da Abubakar Abba ya yi da Shugabar kungiyar koyar da sana’oin hannu ta “Women Skills Initiatibe” resshen jihar Kaduna Hajiya A’isha Gambo ta yi bayanin dalilin da ya sanya mata masu sana’oi a jihar suka yi baje kolin kayan da mata masu sana’oin suka sarrafa da hannu, nasarorin da kungiyar ta samu da sauran su.

Ke ce Shugabar wannan kungiyar wadanne shiye–shirye kuka yi har kuka zo nan wurin?
To, gaskiya shirye-shirye da muka yi suna da yawa, na farko dai mun fara wananan tunanin ne tun lokacin da wannan gwamnatin ta ce a zabura don a zamo masu dogaro da kai, ganin a zaburar sai muka dinga gaya wa mata su ma su zabura. Sai Allah ya taimake mu suka zaburan, a kalla a Kaduna a yanzu muna da cibiyoyi da aka hors da mata sama da dari biyar. To sai ya kasance bayan an yi wa matan horon, ina za su kai kayan nasu don sayarwa? Ba su san inda za su kai su ba, to mu a matsayinmu na masu yi wa matan horo a kan sana’oin na hannu domin dogaro da kansu da kara farfado da tattalin arzikin jihar Kaduna, domin mun riga mun san mata su ne jigon tattalin arziki, domin za ka ga mace ce tun daga cikin gida ta fara yin sana’a sai muka ce to, mai ya kamata mu yi tunda har mun yi wannan yawan a kungiyance da muke yin wannan to mu fito da sana’oinmu mana mu yi baje kolinsu na kwana uku. Idan ya samu karbu wa, duk bayan wata uku ko duk bayan mako biyu ko uku muna baje kayanmu muna samu ana siyarwa to ka ga hakan ba zai sanya su ce sun koya amma ba su san inda za su je su sayar ba.

Amma in an horas da su akwai maganar samar musu da jari, wanne tanadi kuka yi a kan hakan?
To ai don hakan ne muka fito, amma idan muna boye ba wanda zai sanka, amma yanzu da muka fito muka yi magana, har da baje kolin kayan, ka ga ma gwamnati za ta san da mu. Shi ya sa lokacin da muka fara shiye-shiryen mu ba mu fito mun ce gwamnati ta taimaka mana ba domin idan kana so a san lallai kana yi to a gani a kasa.
Ka ga yadda muka fito din nan sai muka kira wo gwamnatin muka ce ta zo ta gani da kuma ku abokan aikinmu ‘yan jarida, kun zo kun ga abin yadda yake, inda mun tafi yawo ne mun ce gwamnati ta zo ta yi mana ba za a fahimce mu ba. Shi ya sa muka fito don a taimaka wa matan da jari, ka ga dai yanzu gwamnati ba ta shigo ba, amma ka ga abin da matan suka yi.
Kamar kungiyoyin matan masu sana’oi nawa ne suka yi baje kolin?
Gasikya sun kusan dari shida.

Amma na ga abin naku kamar ya tsaya ne a cikin birni, kuna tunanin fadada shi zuwa karkara a nan gaba?
In Allah ya so ya yarda, yanzu haka a nan akwai Zariya, Chikun akwai kuma wasu na makwabtanmu, ka san abin da aka ce na farko to dole ne sai a hankali amma nan da wata uku in sha’allahu za mu ci bikin sallah duk za mu sake yin baje kolin.

Me kuke bukata idan gwamnatin ta zo sanya hannu a cikin kungiyar ku?
Abin da muke so ta ba mu jari a bude kamfani wanda idan mata sun yi irin wannan su je saya, a kuma gaya wa ‘yan kasuwar jihar Kaduna su daina tsallaka wa ketare.
Takalma muna da su, jakankuna muna da su, kuma sannan gwamnatin ta kara wa mata ilimi yadda za su kara inganat sana’oin na su.

Wanne kira za ki yi wa sauran kungiyoyin irin naku don su shigo cikin kungiyarku?
Gaskiya duk wata kungiyar da take da abin yi ya kamata ta zo ta shiga don in Allah ya yarda mun riga mun fito ba za kuma mu koma baya ba.

Kuna tunanin fadada wa zuwa fannin noma?
Akwai malamanmu da suke koyar da mu aikin noma domin wasu matan suna yin noman buhu a kofar dakunansu ko yin kiwon kifi duk muna yi ka ga idan gwamnati ta shigo za ta taimaka.

Wato kamar kungiyar ba ta amfana da bashin bankin sana’oi ba da ke bayar da bashin marasa ruwa ga masu sana’oin hannu ba?
Gaskiya ba mu amfana ba.

Amma kun nema?
A toh a yanzu ne a kungiyance muka dunkule amma a da muna wargaje ne amma a yanzu muka dunkiule kungiyar ‘yan kasuwa ta jihar Kaduna ta shigo da ba mu goyon baya dari bisa dari ta ba mu rumfa idan mun gama baje kolin a debi wasu kayan a kai can wanda yake neman ya je can ya same mu.

Exit mobile version