Connect with us

LABARAI

Bikin Nadin Dan Darman Lakwaja Ya Yi Armashi

Published

on

Ranan Asabar, 11 ga Satumba, 2018 rana ce da Barista Nasser Ahmed da masarautar Lakwaja da kuma daukacin al’ummar na Lakwaja ba za su taba manta wa ba a rayuwarsu, domin kuwa a wannan rana ce mai martaba Sarkin Lakwaja, Alhaji (Dr) Muhammadu Kabir Maikarfi Na Uku ya nada tare da tabbatar wa da Barista Alhaji Ahmed sarautar DAN DARMAN Lakwaja.

Bikin wanda aka gudanar a fadar mai martaba Sarkin na Lakwaja, inda aka shirya kasaitaccen hawan daba, ya samu halartan ‘yan asalin garin na Lakwaja daga ciki da kuma wajen jihar Kogi da kuma manyan mutane daga sassa daban daban na kasar nan.

Da yake jawabi jim kadan bayan bikin nadin, mai martaba Sarkin Lakwaja ya ce, ya nadawa Barista Nasser Ahmed sarauta Dan Darman ne saboda muhimmin rawar da yake takawa wajen ciyar da masarautar na Lakwaja gaba.

Mai martaba Sarkin ya kuma yi bayanin cewa, sabon Dan Darman ya bada gagarumin gudunmawarsa wajen bunkasar tattalin arziki da kuma zamantakewar kasar nan a fannoni daban daban inda ake bukatar gudunmawar nasa. Alhaji Muhammadu Kabir Maikarfi har ila yau ya ce, Majalisar Sarakuna na Lakwaja zai ci gaba ka karrama wadanda suka dace da kuma cancanta, inda ya jaddada cewa nadin Barista Nasser Ahmed zai kara wa wadanda suke da sha’awar son nada su sarauta yin koyi dashi. Sarkin na Lakwaja kazalika ya nemi masu rike da rawanin gargajiya daga yankin da su ci gaba da bada shawarwari masu ma, ana ga Majalisar Sarakunan da kuma gwamnati a kan batutuwar da suka shafi jin dadi da walwalar daukacin al’ummar masarautar da kuma na jihar Kogi gaba daya.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai kadan bayan nadin shi, Sabon Dan Darman na Lakwaja, Barista Nasser A Ahmed ya yi alkawarin maido da dimbin tarihi da kuma albarkatun yawan bude idanu (Tourism) na birnin na Lakwaja wanda cibiya ce na zaman lafiya, hadin kai da kuma na addini.

Ya kara da cewa Lakwaja gari ne na zaman lafiya wanda bambancin addini da kabilanci basu da gidin zama ko tasiri. Game da shirya hawan daba kowace shekara a birnin Lakwaja kuwa, Dan Darman yace” Zamu hada hannu da wasu kamfanoni masu zaman kansu domin shiya hawan daba da nufin bunkawa da kuma farfado da darajar birnin Lakwaja tare inganta yawan shakatawa. “Kafin 1960, dukkan masarautar Arewacin Nijeriya suna haduwa a Lakwaja, a don haka bamu ga dalilin da yasa ba za a ci gaba da yin hakan ba “inji shi.

Daga nan ya yi bayanin cewa a yanzu masarautar arewa, musamman wadanda suka binne sarakunansu a Lakwaja sun bashi tabbacin hada kai don shirya kasaitaccen hawan daba a Lakwaja. Har ila yau Dan Darman ya yi alkawarin kafa gidauniyar samar da ilimi domin daukar dawainiyar dalibai yan asalin masarautar Lakwaja dake karatu a manyan makarantun kasar nan inda yace zasu  zuba naira miliyan biyar a matsayin farkon farawa, inda kuma ya tabbatarwa da jams, ar masarautar na Lakwaja kudurinsa na kafa masana, antu tare da samarwa da matasan yankin aikin yi domin maganin zaman kashe wando da suke fama dashi.

Shi dai Barista Nasser A Ahmed, an haifa sane a ranan 29 ga watan maris, 1961 a birnin Kano. Ya yi karatunsa na firamare a makarantar firamare na Gawuna. Daga nan ya zarce kwalejin gwamnatin tarayya dake Kano.

Barista Nasser Ahmed har ila yau ya halarci Jami, ar Ahmadu Bello dake Zaria inda ya yi karatun aikin lauya. Bayan ya kammala ne kuma ya je makarantar koyar aikin lauya (Law School). Ya yi digirinsa na biyu a fannin aikin lauya na kasa da kasa da kuma diflosiyya a Jami, ar Legas.Ya yi aiki a wurare da dama.

A yanzu shine shugaban otel din Central dake birnin Kano .Barista Nasser nada mata da kuma yaya da dama. Cikin mashahuran mutanen da suka halarci gagarumin bikin nadin sarautar sun

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: