Connect with us

LABARAI

Bikin Nadin Kogunan Safana Ya Yi Armashi

Published

on

A ranar 8/9/2018 ne mai girma Yariman Katsina Hakimin Safana, Alhaji Sada Rufa’i ya nada Alhaji Muhammad Abubakar a matsayin Kogunan Safana bisa amincewar mai martaba sarkin Katsina da majalisarsa.

Bayanin tarihin rayuwarsa ya nuna cewa, Alhaji Muhammad Sada ya fara karatun Firamare ne a Gwadabawa, ya kuma yi karatun sakandire a G.S.S Bomo ya kuma wuce jami’ar Ahmadu Bello bayan nan kuma ya yi Masters a jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) kuma ya yi karatutuka a manyan matsayi gida da waje a yanzu haka kuma yana cikin jami’an dake kula da Gidauniyar Sardauna (Sardauna foundation), Yana da mata 2  da yara 8.

Wakilinmu ya halarci wannan gagarumin buki kuma ya ruwaito mana yadda lamarin ya gudana kamar haka. yanuwa da abokan arzuka ne daga sassan kasar nan suka samu halartar taron nadin sarautar wanda jama’ar da suka samu halartar suka nuna jin dadinsu a kan yadda taron ya gudana cikin nasara.

Bayan halartar manyan baki daga masarautar Zazzau da suka hada da wakilci na mai girma sarkin Zazzau da wakilci na Yariman Zazzau Alhaji Manir Jafaru da wakilci daga fadar gwamnatin jihar Kaduna da gwamnatin jihar Nija sai aka dunguma zuwa kasar Safana da ke jihar Katsina don shaida nadin da za a yi wa Alhaji Muhammad Abubakar Saddik.

Tawagar Alhaji Muhammad Abubakar Saddikta isa fadar mai martaba Yariman Katsina Hakimin Safana misalin karfe 11:30 na rana inda aka samu fadar takume da jama’ar arzuki daga bangarorin dangi da mutanen gari manyan baki.

Bayan guri ya cika makil ne mai martaba Yariman Katsina ya bayar da damar a baiwa Alhaji Muhammad Abubakar Saddik damar ya gaisa da manyan baki da suka zo daga bangarensa har zuwa bangaren mai martaba Yariman Katsina.

Bayan an ba da dama kowa ya yi ido biyu da wanda za a nada a matsayin Koguna na Safana, sai aka bai wa majalisar Hakimi da su bada izini a karanta tarihin Alhaji Muhammad Abubakar Daddik kafin a nada masa rawanin sarauta.

Bayan kammala karanta tarihin ne sai mai martaba ya kira Alhaji Muhammad Abubakar ya tsaya a gabansa domin a nada masa rawani a matsayin Kogunan Safana tare da amincewar Sarkin Katsina Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman.

Bayan nada masa rawani ne wakilinmu ya zanta da shi Yariman Katsina Hakimin Safana game da dalilin da ya sa aka yi wa Alhaji Muhammad Abubakar Saddik rawanin Kogunan Safana.

Sai Yariman Katsina ya kada baki ya ce, “Alhaji Muhammad Abubakar Saddik mun bashi wannan sarautar ne bisa cancantarsa da kyawawan dabi’unsa a matsayinsa na dan sarautar tunda ya sami sarautar ne ta kakansa da ke cikin gidan sarautar Katsina kuma Muhammad Abubakar Saddik ya kasance mai taimakon jama’a da samawa masarauta cigaba wanda kuma haka ake so da haka ne muka bashi wannan sarautar kuma muna fatar zai rike amanar masarauta.”

Daga cikin wakilan gwamnati a suka halarci wannan taro akwai wakilin tsohom gwamnan jihar Neja, Alhaji Baba.gida Aliyu wato Alhaji Ham, shima cewa ya yi, “Gaskiya babu abinda za mu ce sai godiyar Allah bisa wannan karamci da aka yi wa shi abokinmu dan haka Allah ya sakawa Yariman Katsina da alkairi Ya kuma taya shi Muhammadu Sadik riko.”

Shi kuwa Alhaji Muhammad Abubakar Sadik a nasa jawabin ya tabbatarwa manema labarai cewa shi ba shi da abinda zai ce face godiya ga Allah, “A kan wannan lamari na bani wannan matsayi dan haka zan yi iyakar kokarina in ga na fitar da masarautar Katsina kunya da shi kansa Yariman Katsina da ya bani wannan matsayi kuma zan yi amfani da wannan dama in godewa duka jama’ar da suka bada goyon baya aka tabbatar da wannan lamari gida da waje, kuma ina fata duk wanda ya zo wannan taro Allah ya mayar da shi gida lafiya.”

Daga cikin baki da suka sami damar halartar wannan waje akwai Wakilin Zurun Zazzau Alhaji Muhammad Usman Mani da Honorabul Muktar Isa Hazo dan majalisar jihar Kaduna mai wakitar Basawa da Sheik Jamilu Al-Bani Samaru, mai bai wa gwamnan Kaduna shawara a kan kungiyoyin addini na jihar Kaduna da Alhaji Suleman Danladi Talban Samaru da kuma Honarabul Shehu Namadi dan takarar kujerar majalisar dokokin jihar Kaduna, an yi taro lafiya an tashi lafiya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: