Umar Faruk" />

Bikin Ranar Cutar Sikili Ta Duniya: Kungiyar Masu Sikila Ta Kebbi Ta Shirya Tsaf

Kungiyar masu dauke da cutar sikila ta kasa reshin Jihar Kebbi ta bayyana shirinta na kaddamar da bukin ranar masu dauke da sikila ta duniya da za ta gudanar a ranar 19 ga watan yuli na shekara ta 2019 a Birnin-kebbi.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugabar kungiyar ta Jihar Kebbi, Hajiya Khadija Yahaya Shantali a lokacin da ta kira taron manema Labarai a ofishinta da ke hanyar Adamu Aliero a unguwar Gesse, da ke Birnin-kebbi a jiya Alhamis.

Hajiya Khadiza Yahaya Shantali ta yi bayanin cewa “kungiyar masu sikila za ta gudanar da zagayen yekuwar fadakarwa kan cutar sikila a cikin garin Birnin-kebbi da kewayenta tare da wasu kungiyoyi masu zaman kansu don kore cutar laulayin kashi a duk duniya. Haka kuma mun zabi makarantun firamare da na sakandare na cikin garin Birnin-kebbi don zuwa a wayar da kansu kan cutar sikila da wasu mutane ke fama da su.”

   Har ilaya shugabar ta ce “a ranar 18 ga watan na yulin wannan shekara da muke cikin kungiyar tare da shuwagabannin babban Bankin Nijeriya za su gudanar da bikin kaddamar da dakin gwaji na masu cutar sikila da ma wadanda ba su dauke da cutar wanda babban bankin ya basu a matsayin gudunmuwarsu don taimaka wa jama’ar da ke dauke cutar. Kungiyar sikila ta aike wa Sarkin Gwandu, gwamnatin Jihar Kebbi da kuma dukkan masu ruwa da tsaki kan harakar kiyon Lafiya a jihar ta Kebbi da kuma wajen ta domin halarta,” in ji ta.

Bugu da kari, Hajiya Kahadija ta ce a ranar 19 ga watan Yulin bayan gudanar bikin na duniya bakin daya, sun shirya gasar kacici-kacici ga wasu makarantun sakandare don ilmantar da su kan illoli da kuma hanyoyin da za a iya magance matsalolin cutar ta sikila. Inda ta ce duk makarantar da ta samu nasarar zama ta daya da ta biyu har zuwa ta uku za su karbi kyautar kofi da aka sanya wa suna “Rugums Cups” don tunawa da mahaifinta Dakta Yahaya Shantali, Sarkin Shanun Gwandu, wanda ake yi wa lakabi da “Rugum uban ‘yan boko”.

Exit mobile version