Bikin Sallah Babba: NSCDC Ta Tura Jami’ai 2,500 Domin Ba Da Tsaro A Kaduna

NSCDC

Pic.3. Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) personnel training in preparation for the 2019 General Elections in Port Harcourt on Monday (18/2/19). NSCDC have deployed 60,000 personnel nationwide for the elections. 01489/19/2/2019/Chidi Ohalete/BJO/NAN

Daga Rabiu Ali Indabawa

A kokarin da take na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a Jihar Kaduna musamman a wannan lokaci na bukukuwan Babbar Sallah, kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya Cibil Deffece na Jihar Kaduna, ya ce ya tura sama da ma’aikata 2,500 domin bikin Sallah Babba na bana. .

Tura dakarun, a cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar (CPRO), DSC Orndiir Terzungwe, wanda yake a bayyane, ya shafi dukkan kananan hukumomi 23 na jihar kafin lokacin da kuma bayan gudanar bikin.

Ya ce Kwamandan Jiha, Godwin Miebi, ya umarci runduna ta shiyya ta hanyar Kwamandojin yankin da ke tattara dukkan abubuwan da za su tattauna game da haduwar da za su yi tare da yi musu bayani kan yadda za a yi aiki a kan wuraren da suka mamaye domin samun kyakkyawan sakamako.

Haka zalika, dukkannin shugabannin sassa da bangarorin da ke hedikwatar Jihar an tattara su karkashin sashin ayyuka, an yi musu bayani kuma an aika su wuraren da suka kamata.

An ruwaito Kwamandan yana cewa, “a cikin lokacin da ake la’akari da shi na rashin tsaro, za a dauki tsauraran matakan sa ido na masu tafiyar kafa da sintiri na ababen hawa da nufin kare Dukiyar Kasa da Muhimman abubuwan more rayuwa daga masu aikata miyagun laifuka.

“Jami’an da ke aiki a sashen yaki da masu aikata barna, sashen yaki da ta’addanci, sashen leken asiri da sauran rundunoni, an tattara su yadda za su yi aiki tare da sauran hukumomi.”

Ya kara bayyana cewa idan aka samu cikakken hadin kai daga jama’a, ko shakka babu hakan zai magance barazanar tsaro da ya shafi jihar, maimakon barin aikin ga hukumomin tsaro kawai. Yayin da yake kira ga mazauna jihar da su rungumi zaman lafiya da juna, Kwamandan ya taya murna tare da gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai, mataimakinsa, mambobin majalisar zartarwa ta jihar da kuma majalisar dokoki da mutanen jihar a ranar Idi ta bana.

Exit mobile version