Bello Hamza" />

Bikin Sallah: Shugaban Majalisar Nasarawa Ya Nemi Yin Addu’o’in Kawo Karshen Cutar Korona

Shugaban majalisar dokokin jihar Nasarawa, Alhaji Ibrahim Abdullahi, ya bukaci al’umma su rungumi addu’o’in na ganin an kawo kashe matsalolin tsaro da kuma cuta korona a fadin tarayya kasar nan.
Alhaji Abdullahi ya yi wannan kiran ne sanarwa da ta fitio daga jami’in watsa labaransa, Jibrin Gwamna, a garin Keffi ranar Juma’a.
Shugaban Majalisar ya taya al’umma Musulmi murnan bikin Sallah ya kuma bukace su da su mika hannun taimako ga sauran al’umma marasa galihu koda kuwa ba addininsu daya ba.
Ya kuma ce, ya kamata Musulmi su nuna soyayya ga ‘yan uwansu ‘yan Nijeriya don ta haka ne za a tabbara da cigaban kasar da bunkasarta.
Ya ce. Addu’a ita ce babbar makamin al’umma a halin yanzu, don haka yakamata a cigaba da yi wa kasa addu’a a dukkan lokaci.
Ya kuma bukaci al’umma su gabatar da adduo’in neman kawo karshen annobar cutar korona da kuma neman kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi wasu yanki na kasar nan, daga nan ya nemi al’umma su rungumi dukkan matakai da masana suka samar na kariya daga cutar korona.
Shugaban majalisar ya kuma bayar da tabbacin aiki tare da bangaren zartaswa don ciyar da jihar Nasarawa gaba.

Exit mobile version