Bikin Sallar Bana Ba Na Masha’a Ba Ne, Na Addu’o’i Ne Kan Tsaro – Gwamnan Neja

Daga Muhammad Awwal Umar,

Gwamnan Jihar Neja kuma shugaban kungiyar gwamnonin arewa ta tsakiya, Abubakar Sani Bello ya taya al’ummar musulmi murnar bukin sallar Idil-fitir na shekarar 2021 bayan kammala azumin watan Ramadan lafiya.

Gwamnan ya yi kiran ne a wata takardar manema labarai, da sakatariyar yada labaransa Mary Noel Berje ta fitar. Gwamnan ya ce bukin sallar ba na masha’a ba ne, buki ne na yin addu’o’i dan kawo karshen matsalar tsaro a jihar da kasa baki daya.

Gwamna Sani Bello, ya jawo hankalin al’ummar musulmi da su yi koyi da darussan da suka koya a lokacin azumin watan Ramadan, kuma su yi aiki da imanin da suka samu wajen canja dabi’unsu dan samun al’umma nagartacciya.

” Ina kira ga dukkan musulmi da su yi koyi da darussan wajen daidaita rayuwar su, horarwa da kyautatawa da suka koya a watan Ramadan, kuma su kaucewa shaidanu da shaidanci wajen gurgunta jihar da kasa baki daya”.

Ya nuna yakininsa akan ibadun da aka yi daidai da gafarar da aka nema a cikin watan zai zamo jagora har karshen shekarar wanda zai kawo karin cigaba daga Allah madaukaki.

Gwamnan ya yi amfani da wannan damar wajen jawo hankalin al’ummar jihar da su kara imani da baiwa gwamnati goyon baya a kokarinta na samun mafita da matsalar rashin tsaron da ya shafi jihar da kasa baki daya.

Ya ce gwamnatin jihar tana sane da matsalolin da ke tasowa a kan matsalar tsaro a wasu sassan jihar kuma yanzu haka gwamnatin jihar na aiki tare da hadin guiwar jami’an tsaro, dan karya lagon ‘yan ta’addan da kuma ganin dukkanin ‘yan gudun hijira sun koma gidajen su.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa tana kokarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a kuma tana kara ba da tabbacin za ta taimaka wa ‘yan gudun hijira har sai sun koma gidajensu dan cigaba da rayuwa mai inganci.

Ya taya al’ummar musulmi murnar sake samun damar ganin wani sallar Idil-fitir, gwamnan ya nemi al’ummar da su yi anfani da wannan lokacin wajen yin addu’o’in samun hadin kai, zaman lafiya da cigaban kasa.

Haka ya nemi musulmi da su cigaba da koyi da darussan da suka koya a lokacin Ramadan, ta hanyar kyautatawa makota dan zaman lafiya, tsaro, tattalin arziki da cigaban kasa a jihar da kasa baki daya.

Exit mobile version