CRI Hausa" />

Bill Gates: Sin Ta Saukakawa Duniya A Fannin Yaki Da Sauyin Yanayi

Mallakin kamfanin fasaha na Microsoft Mr. Bill Gates ya jinjinawa kwazon kasar Sin, don gane da daukaka matsayin ayyukan kyautata yanayi da kasar ke aiwatarwa, da kuma irin gudummawar da kasar ta bayar wajen rage fitar da iskar carbon. Ya ce duniya ta amfana daga himmar Sin, wajen saukaka samar da makamashi maras gurbata muhalli mai araha.

Da yake karin haske kan hakan, yayin tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Mr. Gates ya ce abu ne mai kyau, ganin yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya dauki batun kare muhalli da matukar muhimmanci, yana kuma fatan aiki da sauran abokan hulda na kasa da kasa a fannin.
Bill Gates ya ce, kasar Sin na fatan kaiwa karshe matsayin fitar da iskar CO2 kafin shekarar 2030, tare da cimma matsayin kawar da fitar da wannan nau’i na iska kafin shekarar 2060, kamar dai yadda shugaba Xi Jinping ya bayyana, yayin babban taron MDD karo na 75, wanda ya gudana ta kafar bidiyo a watan Satumbar bara.
Kaza lika a cewar sa, Sin ta sassauta farashin makamashin lantarki ta hasken rana, da motoci masu amfani da lantarki, ta yadda al’ummun duniya ke iya sayen su, yayin da amfani da motoci kirar Bas masu amfani da lantarki ke kara yawaita a biranen kasar.
A daya bangaren kuma, Sin na yin dukkanin mai yiwuwa, wajen samar da turakun lantarki na caftacaccen makamashi. Daga nan sai ya yi fatan ganin Sinawa masu kirkire kirkire, sun kara saukaka farashin sassan makamashi mai tsafta, ta yadda kasar Sin za ta kara ba da gudummawa ta fuskar cin gajiya, daga nau’o’in makamashin mai tsafta, karkashin shawarar nan ta ziri daya da hanya daya. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)

Exit mobile version