Connect with us

RIGAR 'YANCI

Bilya Bawale Ba Shi Da Kudurin Takarar Mukamin Siyasa – Manpower

Published

on

Sakataren kungiyar Bilyaminu Bawale Foundation Malam Zubairu Abubakar (Manpower) ya bayyana cewa Alhaji Bilyaminu Bawale Babban hadimin shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattijai watau Sanata Dokta Yahaya Abdullahi ba shi da kudurin takarar kowane irin mukamin siyasa.
Ya yi wannan bayani ne a wata zantawa da wakilinmu a garin Argungu da ke jihar kebbi inda ya bayyana cewa bisa ga irin ayuka da kuma gudummawa da ya ke bayarwa ga al’umma a duk lokacin da wata bukata ta taso ne ya sanya wadansu mutane ke ganin kamar yana da kudurin takarar wani mukamin siyasa wanda sam ba haka ba ne. Magana ta gaskiya dai ita ce a matsayinsa na daya daga cikin matasan da Allah ya kai su ga wani bagire ne ya ke ganin yana da kyau shi ma bayarda tasa gudummawa wajen ciyarda yankinsa gaba.
Ya cigaba da cewa sau da yawa kungiyoyin matasa dabam-daban sun sha tuntubarsu dangane maganganun da ke yawo ana  yayata cewa Bilya yana da kudurin takara amma su kan gaya musu da cewa ba gaskiya ba ne illa dai yana karfafa siyasar maigidansa ne watau Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattijai watau Sanata Dokta Yahaya Abdullahi mai wakiltar  gundumar Kebbi ta Arewa.
Kowa yana da ikon ya fadi albarkacin bakinsa ko ra’ayinsa ko kuma irin nasa hasashen amma bai zamo lallai hasashen ya kasance gaskiya ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: