Connect with us

Madubin Rayuwa

Bincike A Tsakanin Maza Da Mata: Wa Suka Fi Cancanta Da Shugabancin Siyasa?

Published

on

Wannan Makala Tawa Ta Yau, Makala Ce Mai Taken: Tsakanin Maza Da Mata Su Waye Su Ka Fi Cancanta Su Shugabanci Al’umma A Tsarin Shugabancin Siyasa? Na Kawo Cikakken Bayanin Rahoton Sakamakon Wani Bincike Da Wata Cibiya Ta Gudanar A kasar Amurka Kan Amsar Wannan Tambaya.
Tun da farko, rahoton binciken ya bayyana cewa Amurkawa sun yi imanin cewa hakika mata sun cika dukkan wani kwaliti na cancantar su zama shugabanni a kan doron tsarin shugabancin siyasa. Duba da gaskiyarsu da kwarewarsu da kuma kaunarsu ga al’umma. A wani rahoton binciken jin ra’ayin jama’a na kasa gaba daya wanda cibiyar bincike ta gudanar a kasar Amurka, mata ne su ka hau sahun gaba ta fuskar cancantar yin shugabancin siyasa sama da maza.
A rahoton wannan bincike da aka fitar, sakamakon ya nuna cewar kashi shida (6%) na mutane (2,250) da aka ji ra’ayinsu sun bayyana cewa mata sun fi cancantar su zama shugabannin siyasa fiye da maza. Sannan mutum daya cikin mutane biyar, kashi (21%) sun bayyana cewa maza sun fi mata cancantar zama shugabannin siyasa. A ra’ayi na bai daya kuma, kaso sittin da tara (69%) sun bayyana cewa babu bambancin kwaliti (nagarta) ta fuskar cancantar shugabancin siyasa a tsakanin maza da mata, gaba daya kwalatinsu (nagartarsu) daya ne maza ba su fi mata ba, mata ma ba su fi maza ba.
Bayan wannan kuma, a fannonin awun kwalitin shugabanci bakwai daga cikin takwas da aka auna daga ra’ayoyin na jama’a, al’umma sun bayyan cewa idan har mata ba su fi maza ba, to za su zamto daidai da daidai su ke. Misali, cikakkun mutane masu hankali (balagaggu), akasari gaba dayansu sun shaida cewa mata sun fi maza gaskiya (Honesty). Yan kalilan ne su ka bayyana cewa babu wanda ya fi wani kan gaskiya ta fuskar shugabanci a tsakanin jinsinan guda biyu, (maza da mata). Kuma gaskiya ita ce mahanga ta farko a fagen awun sikelin cancantar shugabanci kamar yadda ra'ayin na jama'a ya bayyana.
Sannan ma'auni na biyu kuma shi ne fikira da kwarewa, a wannan ma'auni ma mata sun yi wa maza fintinkau, domin kuwa rahoton binciken jin ra'ayin jama'ar ya tabbatar da cewa kaso talatin da takwas (38%) na mutanen da aka ji ra'ayinsu sun bayyana cewa mata sun fi maza kwarewa ko hikima da fikira (Intelligence), kaso goma sha hudu (14%) kuma su ne su ka ce maza sun fi mata, ya yin kuma da sauran kason su ka ce babu wanda ya fi wani a tsakanin mazan da matan.
A cikin fannonin takwas na auna kwalitin cancantar shugabanci tsakanin maza da mata, a fannin zaman Ofis a jima ana aiki ne kawai binciken ya nuna cewa maza sun fi mata aiki tukuru inda sakamakon rahoton jin ra'ayin jama'ar ya bayyana cewa maza sun samu kaso arba'in da hudu (44%) ya yin kuma da mata su ka samu kaso talatin da uku (33%) na ra'ayin jama'ar.
A sakamako na gaba daya kuwa, ra'ayin jama'a ya bayyana cewa mata sun fi maza kan wadannan ma'aunai guda uku, domin kuwa kaso tamanin (80%), sun bayyana cewa mata sun fi maza, sai kaso biyar (5%), da su ka ce maza sun fi mata, ya yin kuma da a fannin kirkira kaso sittin da biyu (62%), su ka ce mata sun fi maza, kaso sha daya (11%) kuma su ka ce maza sun fi mata.
A duk wannan kididdiga, mata sun rinjayi maza, inda kaso biyu cikin uku na yawan jama'ar maza da mata da su ka shaida cewar mata sun fi maza kwaliti da nagartar jagoranci a doron siyasa. Dadi da kari, a sashen tafikar da harkokin mulkin sassan fannonin rayuwar al'umma kamar kiwon lafiya da ilimi nan ma mata sun fi maza, ya yin kuma da maza su ka fi nata a fannin tafikar da yaki da manyan laifuka da aikin tsaron kasa. Sannan a fannin kiyaye gaskiya da adalci kan harkokin gwamnati da jure adawar siyasa da kaifin basirar gudanarwa cikin kare hakkin al'umma kuwa nan ma ra'ayin na al'umma ya bayyana cewa mata sun fi maza. A sakamako na baidaya kuma, kaso (69%) na mutanen da aka ji ra'ayin nasu sun bayyana cewa duk kwalitin shugabancin siyasa daya ne a tsakanin maza da mata babu wanda ya fi wani.
Sai dai kuma duk da haka abin takaici ga mata, kaso biyu (2%) kawai mata su ke da shi na jagoranci (COE), a kamfanonin 500 a kasa. A sashen siyasa kuwa kaso sha bakwai (17%) su ke da shi a zauren majalisissar wakilai ta Amurka ya yin kuma da su ke da kaso sha shida (16%) a zauren Majalissar Dattijai na Amurka da kuma kaso sha shida (16%) na gwamnoni. Sai kuma kaso ishirin da hudu (24%) da su ke da shi na
yan majalissa gaba daya. Sai dai sakamakon rahoton jin ra’ayin jama’ar game da dalilan da su ka sanya ba a ba wa mata dama yadda ya kamata a kasar Amurkan ya nuna cewa Amurkawa ba su shirya zaɓen mata akan manyan kujerun siyasa ba, kamar yadda aka fahimci hakan daga kaso hamsin da daya (51%) na al’ummar da su ka bayyana ra’ayinsu. Sai dai kuma sama da mutane hudu cikin goma, kaso arba’in da uku (43%), ra’ayinsu ya karkata kan cewa babban dalili shi ne mafi yawan gogaggun mata `yan siyasa maza ne su ke tsaya musu a baya. Ya yin kum da kaso talatin da takwas (38%), su ka bayyana cewa wariya ake nunawa mata a kan kowane fanni na rayuwa ciki har da siyasa.
Advertisement

labarai