Daga Abdulrazaƙ Yahuza Jere, Abuja
Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya tabbatarwa da ’yan Nijeriya cewa, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari mutum ne mai kima da martaba da ba zai taɓa tsoma baki game da batun badaƙalar da ake zargin an tafka a Kamfanin Mai Na Ƙasa (NNPC) ba.
Wamakko wanda shi ne shugaban Kwamitin Karatun Elemantare da Sakandare na Majalisar Dattawa, har ila yau shi ne kuma yake shugabantar kwamicin wucin-gadi na majalisar da aka ɗora wa alhakin binciken badaƙalar.
Da yake jawabi a yayin ƙaddamar da aikin kwamitin a Abuja, Sanata Wamakko ya ƙaryata raɗe-raɗin da ake yi cewa wai ana matsa musu lamba kan lamarin.
‘’Bari in ƙaryata raɗe-raɗin da wasu ke yaɗawa cewa wai kwamitin nan yana shan matsin lamba walau daga fadar shugaban ƙasa ko wani wuri daban. Gaskiyar magana ita ce babu wanda yake matsa mana lamba daga ko ina, ballantana fadar shugaban ƙasa.
“Ina tabbatar muku da cewa mu da muka san Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari muna da tabbacin cewa ba zai taɓa tsoma baki a kan ire-iren waɗannan abubuwan ba”, in ji Wamakko.
Sanatan ya ce an samu jinkirin ƙaddamar da aikin kwamitin ne saboda Shugaban Majalisar Dattawa ya yi tafiya zuwa waje tare da wasu mutane da suke da muhimmanci a cikin kwamitin na wucin-gadi.
Ya ƙara da cewa, “Sun yi tafiya zuwa Ƙasar Rasha tare da Shugaban Majalisar Dattawa kuma suna da matuƙar muhimmanci a cikin kwamitin nan”.
Idan ba a manta ba, a kwanan baya ne Ministan mai Kachikwu ya zargi Shugaban NNPC Baru da bayar da kwangiloli na bilyoyin Naira ba tare da bin ƙa’ida ba, zargin da shugaban kamfanin ya ce bashi da buri balle makama.