Binciken Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Kaso 83.1% Na Masu Amfani Da Intanet Suna Goyon Bayan Binciken Asalin Annobar COVID-19 A Amurka

COVID-19 A Amurka

Daga CRI Hausa,

A daren ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata, cibiyar kwararru ta CGTN,  ta fitar da tambayoyin binciken ra’ayoyin jama’a a wasu dandalin sada zumunta, ciki har da YouTube, Twitter, Facebook, Contact, Weibo, da WeChat a cikin yaruka shida na Majalisar Dinkin Duniya.

Sakamakon amsoshin da suka bayar, masu amfani da Intanet a kasashe daban daban, sun lura da irin wadannan hakikanin abubuwan, wato tun daga watan Yuli na shekarar 2019, an samu yaduwar cutar numfashi da ba a san dalili ba a jihar Virginia ta kasar Amurka, kuma an samu barkewar cutar “huhu ta e-sigari” a jihar Wisconsin ta kasar, kana kuma a wannan wata na Yuli, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Amurka ta rufe dakin gwaje-gwaje na halittu na Detrick ba zato ba tsammani.

Daga watan Disamban shekarar 2019 zuwa watan Janairun shekarar 2020, a cikin samfuran da aka adana na gudummawar jini na yau da kullum na jihohi 9 a Amurka, abubuwan dake yaki da cutar COVID-19 na jikin mutane guda 106 sun nuna alamar kamuwa da cutar. Don haka, kashi 83.1% na masu amfani da Intanet wadanda suka shiga jefa kuri’ar sun ba da shawarar cewa, ya kamata hukumar WHO ta binciki Amurka.

Masu amfani da Intanet na kasa da kasa da ke magana da yaruka daban daban, duk suna barin tsokaci iri daya. Wani mai amfani da Intanet da ke magana da Ingilishi ya ce, “Muna goyon bayan binciken da hukumar WHO za ta yi kan Amurka. Bai kamata hukumar ta dauki ma’auni biyu ba, domin WHO tana wakiltar duniya ne ba Amurka kadai ba. Wadanda ke kara tuhumar wasu suna da abubuwa masu yawa a boye.”

Cibiyar masana ta CGTN ta gano cewa, masu amfani da Intanet sama da 81,600, da suka halarci binciken ra’ayoyin na wannan zagaye, gaba daya sun nuna rashin yarda da rashin gamsuwa kan Amurka. Wanda aka fi nunawa wajen daukar ma’auni biyu, yayin fuskantar matsalolin wasu kasashe da na cikin gida, kana da nuna raini, da siyasantar da batun gano asalin cutar, da kara nuna bambanci da haifar da tashin hankali a kan mutanen Asiya dake kasar bayan barkewar cutar. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

Exit mobile version