Binciken Wayoyin Mata Laifi Ne A Kasar Saudiyya

Miji ya duba abubuwan dake cikin wayar matar shi yanzu laifi ne a kasar Saudiyya, za kuma ayi ma shi tarar dala 133,009, da kuma shekaradaya a gidan kurkuku, a wata sabuwar doka wadda aka yi domin,’’ A kare damar da kowa yake da ita a cikin al’umma da kuma kare’yanci’’.

Wannan dokar za ta shafi dukkan maza da mata adanda suke zaune  a gruruwan da muslmai suke.

Wannan doka za ta kare maza ne daga matansu, kamar yadda abin yake a ksashen musulmai, dokar sakin aure a kasar Saudiyya kamar yadda take cikin Alkur’ani mai girma,sau da yawa, tana bukatar mata su, bayar da shaida akan, yadda aka danne hakki.

Wayar miji kuma nan ne za a iya samun hujjoji masu karfi wadanda za  aiya amfani dasu, wajen daukar wani mataki.

Dokar Anti- Cybercrime wato laifin da ya shafi hanyoyin sadarwa na zamani da nuna cewar, ‘’Kallo, kwacewa, ko amfani data ta abokin zama, ta hanyar samar da dama ta network, ko kuma komfuta, ba tare da izni ba, babban laifi bane’’.

Wannan laifi akwai hukuncin dalar 133,000 ko kuma daurin shekara daya gidan kurkuku ko kuma a hada duka.

Hanyoyin sadarwa na zamani sun kasance wani wuri ne na aikata laifuka, da suka hada da sharri, almubazzaranci, ga ma wani sharri, wannan ma ya hada da amfani da account din wani,kamar yadda ma’aikatar ta jaddada.

Irin wannan doka makwabciyar kasar wato hadaddiyar daular Larabawa  wato United Arab Emirates,ana iya daure mutum watanni uku da kuma biyan dala 817.

Kasar mai arzikin manfetur da wasu kasashe wadanda suka fi amfani da hanyoyin sadarwa na zamani a duniya, amma kuma amfani da al’adu, na kawo masu cikas akan amfani da hanyoyin.

 

Exit mobile version