Yusuf Shuaibu" />

Binuwe: ’Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Uku Da Raunata Dan Jarida

A ranar Litinin ce, wasu ‘yan bindiga su ka kashe mutum uku tare da raunata wani dan jarida, a kan hanyar Kastina-Ala zuwa Ugbema cikin karamar hukumar Kastina-Ala cikin Jihar Benuwe. Majiyarmu ta labarta mana cewa, shi dai dan jaridan mai suna Benjamin Agesan, ya na aiki ne a gidan jaridar Business Day Newspaprs da ke cikin Jihar Benuwe, ya na cikin tafiya tare da mamatan lokacin da ‘yan bindigar su ka bude wa motarsu wuta.
Wani aminin dan jaridan wanda a ka raunata mai suna Jerry Iorngaem, ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne kilomita biyar da garin Kastina-Ala. Iorngaem ya kara da cewa, dan jaridan ya na dawo ne daga garin Makurdi zuwa Kastina-Ala, a cikin motar bas din haya tare da sauran ‘yan jarida lokacin da lamarin ya afku. Ya ce, bayan ‘yan jaridan akwai jami’an amsar haraji a cikin wannan bas din tare da makudan kudade, inda ‘yan bindigar su ka biyo wannan kudi. Iorngaem ya cigaba da cewa, ‘yan bindigar su na biye da motar lokacin da ta tashi tun daga garin Makurdi, inda su ka bude wa motar wuta mintina kadan da tashin motar, sun dai kashe mutum uku nan take tare da yin awon gaba da makudan kudade. Ya ce, dan jaridan ya samu mummunan raunin harbin bindiga a cikinsa, kuma a halin yanzu ya na jiya a asibiti.
Lokacin da wakilinmu ya tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Benuwe, Catherine Anene, ta bayyana cewa, ba ta samu lamari makamancin wannan ba.

Exit mobile version