Daga Balarabe Sulaiman Kafinta
Babban Birnin Tarayya Abuja, gari ne da ya shahara a duniya, sakamakon irin tsarin taswirar da aka yi masa, har ila yau birni ne yake janyo hankalin hatta ‘yan Nijeriya, wadanda suke da burin yin rayuwa irinta kasaita. Hakan ya faru ne sakamakon kasancewar gari ne na mulki. Gari ne wanda ya sha bamban da sauran birane na Nijeriya saboda shi tsara shi aka yi tun daga farko.
Abuja an tsara ta ne domin gudanar da mulkin Tarayyar Nijeriya da ya maye gurbin birnin Ikko, sakamakon cunkushewa da ya yi.
Shugaban kasar soji Janar Murtala Muhammad a watan Augusta na shekarar 1975 ya kafa kwamiti a karkashin Maishari’a T. A. Aguda domin ya nemo wurin da ya dace a gina sabon birnin Tarayya.
- Ya zamanto yana tsakiyar Nijeriya
- Yanayi mai kyau.
- Girman kasa
- Samuwar ruwan da zai iya shayar da mutanen garin
- Tsaro
- Ya kasance ba kabilar da za ta yi ikirarin kasar ta ce.
- Kuma ya kasance wurin ba zai ba da wahala ba wajen ginawa.
Abuja ba shi ne kadai garin da aka duba ba, wannan kwamitin ya duba garuruwa kamar su Makurdi, Okene, Kafanchan, Auchi, da sauran garuruwa da suke a tsakiyar Nijeriya. Abuja ce aka ga ta cancanta da wadannan sharuda duk da yake dai akwai kabilu da suke zaune a wannan wuri kafin wannan lokaci wadanda a yanzu suna korafin ana musu danniya.
Tarihin Abuja ya nuna tana daga cikin masarautar Zazzau ne kafin zuwan turawan mulkin mallaka. Shi kan shi sunan Abuja ana ikirarin an samo shi ne daga sunan Abu Ja (sunan sa Abubakar an hada da lakabin ja saboda hasken fatarsa) wanda kani ne ga Muhammadu Makau Sarkin Zazzau, wanda Fulani suka kora sakamakon jihadi, sai suka yi kaura zuwa Abuja suka kafa mulki. A shekarar 1825, Abu Ja ya gaji mulkin wannan masarauta daga wajen ‘ya’yansa, garin Suleja a yanzu shi ake kira da Abuja a wancan lokaci amma masarautar ta hada da wasu yankunan Abuja ta yanzu.
Lokacin da aka zabi wurin da za a gina birnin Tarayya shi ne aka aro sunan wannan masarauta aka bawa birnin Tarayyar saboda muhimmancin masarautar ita kuma ta sauya suna zuwa Suleja. Shi garin Suleja yanzu yana cikin jihar Neja ne, ita kuma Abuja ta yanzu an hado ta ne daga yankunan jihohin Neja, Kogi da Nassarawa.
Mutanen da suka fi yawa a wannan yanki su ne Gbagyi wadanda aka fi sani da Gwari, sai kabilar Koro, Gade, Egbura, Gwandara, bassa da kuma Ganagana.
Tsarin mulkin kasa ya rarraba Abuja zuwa hiyyoyi shida (6) wadanda suke a matsayin kananan hukumomi. Dukkaninsu suna karkashin hukumar gudanarwa ta birnin Tarayya (FCTA) su ke. Ita wannan hukuma tana karkashin Ministan Birnin Tarayya wanda shugaban kasa ye ke nadawa domin gudanar da mulkin yankin birnin tarrayyar a madadinsa.
Ga wanda bai taba zuwa Abuja ba zai ta tsammani idan yaje wannan gari zai samu yanayi irin na kasashen da suka ci gaba a duniya saboda irin labaran da ake yadawa game da Abuja din. Lallai kam farkon zuwan mutum Abuja zai ga bambanci tsakanin garin da sauran jihohi. Akwai manyan tituna da gine gine da wuraren shakatawa. Ko wace gunduma tana da babban asibiti. Misali akwai asibitin Wuse, Maitama, Asokoro da Garki. Wutar lantarki ba ta cika yankewa ba idan kanan cikin garin Abuja haka ma ruwan famfo.
Tituna da suke cikin gari ba su da cunkoso saboda girman da suke da shi. Misali titin da zai kai ka daga cikin gari zuwa zuba yana da fadin da mota biyar za su iya jerawa su yi ta gudu a tare ba tare da wani ya gogi wani ba. Haka idan ka shiga cikin unguwanni za ka gan su kalkal gwanin ban sha’awa. Kwatocin su duk a rufe suke, kuma da an yi ruwan sama suke shanyewa ba tare da samun ambaliya ba. Maganar sauro kuwa babu ba wurin fakewarsu. Ga gidaje manya-manya gwanin ban sha’awa sun sha ado da bishiyu da furanni.
Tsarin garin ya tanadarwa ma’aikata manya da kanana gidajen zama. A unguwannin Garki da Wuse nan gidajen ma’aikata suka fi yawa saboda kusancin su da ma’aikatu. An gina gidajen ne masu daki daya, masu daki biyu da kuma masu daki hudu. Amma wani abin takaici a halin da ake ciki yanzu, tsakanin karamin ma’aikaci da wadannn gidajen sai dai kallo. Wannan ya faru ne sakamakon sayar da gidajen da gwamnati ta yi ga masu karfin siya. Kananan ma’aikata kuwa sai dai su nemi wurin zama a gefen gari ko kauyuka da suke kewaye da birnin.
Duk inda aka ce kujerar mulkin kasa take, to wannan wuri zai zama kamar wani mayen karfe ne dake janyo mutane gare shi. Mutane kowa son zuwa Abuja yake. Idan da za ka shiga jami’oi a kasar nan ka tambayi dalibai, za ka ji burinsu bai wuce su sami aiki a Abuja ba. Idan muka koma kauye kuma, Abuja ya zama burin ko wane saurayi da yake da niyyar zuwa ci-rani domin neman abinda zai rufawa kan sa asiri.
Ba a nan gizon yake sakar ba, babban kalubalen da mutum zai fara fuskanta idan har ya dace ya samu abin yi a Abuja shi ne matsalar wurin zama. Muhalli ya fi komai daraja sakamakon duk wani wuri da aka tanada don masu karamin karfi an sayar da shi ga masu ikon siya kuma a halin yanzu farashin siya ko haya ya fi karfin babban ma’aikaci in dai ba yana hadawa da ‘yan buge-buge ba.
Masu kananan sana’oi ma ba a maganarsu domin su kam mafi yawa sai dai su tafi garuruwa irin su Suleja ko kauyukan dake kewaye da birnin Abuja kamar su Mpape, Karmajiji, Gishiri, Kurundumau, Kabusa, Dei-Dei da sauransu.
Masu sana’a kuma wadanda basu da halin biyan mota zuwa wurin ayyukansu (tun da akalla mutum ya kashe N300 zuwa N600 kullum a mota kawai banda kudin abinci) sai dai su makale a wuraren da ake kira billage (kauye ke nan a hausance) wanda suna tsakar garin Abujan ne kuma wuri ne na ‘yan asalin Abuja. Za ka same su suna ta gararamba a cikin wadannan kauyukan idan sun taso daga aiki. Su ne hira a teburin mai shayi, ko kuma ka gan su kewaye da masu abinci ana ta zolayar ‘yan mata ko kuma ka gan su suna taya mai nama hira. Wani lokaci kuma ka gansu sun yi da’ira ana kallon fim a waya. Lokacin bacci yana yi sai ka ga kowa ya nemi kofar shago ya shimfida ‘yar leda ko tabarma ya kwanta har zuwa wayewar gari. Masu turin baro kuma ka gansu sun dunkule cikin barukansu suna bacci abinsu. Abin takaici kuma mafi yawansu suna da gida a kauyukansu manya-manya ko da ba na zamani ba ne. Kuma suna da gonaki amma sun baro saboda suna hangen Abuja.
Tabbas a wani kaulin za a iya cewar Abuja marmari ce daga nesa, saboda gari ne da ake labarin kyawunsa, kuma ana ganin cewa ya zama dole ya yi kyau din kasancewarsa birnin mulki. Amma da zarra ka sanyan kafarsa sai ya lamari sha bamban.
A tsakiyar garin Abuja, akwai gidajen kasa, kuma ana sayar da ruwa a jarkoki kamar ko’ina a Nijeriya. Misalign irin wadannan unguwanni su ne, Garki Billage, Asokoro Billage, Jabi Daki Biyu, Gishiri, Mabushi da dai sauran su.
Daga gefe kuma za ka iya samun unguwanni kamar su Mpape, Nyanya, Karmajiji, Dakwa da dai sauransu. Duk wadannan garuruwa da na lissafo babu inda ake da wani cikakken tsari na magudanar ruwa, babu titi, babu ingantattun makarantu. Kusan Garki kadai za a iya cewa suna da ruwan famfo.
Wani babban abin mamki kuma za ka ga cewa mutanen da suke a wadannan unguwanni ba su samun kulawa sosai daga gwamnati duk da cewa an zo an same su ne kuma sun sadaukar da garinsu sun rungumi sauran ‘yan Nijeriya da suka zo aiki ko san’a.
Bari mu dawo wurin ma’aikata musamman na gwamnati. Sun fi kowa zama abin tausayi a jerin mazauna Abuja. Dalilin fadin hakan shi ne, sun baro gida da dogon buri ana ganin shi ke nan kudin ya zo. Bayan wasu ‘yan watanni wannan tunanin zai canja saboda zai ga cewa kudin mota da na abinci ma kadai ya ishi mutum. Idan kuma ya fara biyan haya to a nan ido zai raina fata. Gida mai daki biyu a cikin gari kamar irin su Wuse, Jabi, Garki ya fara ne daga miliyan daya (N1,500,000) zuwa sama. Ka ga kuwa wanda yake matakin albashi na sha biyu (gl 12) ma wannan farashin ya fi karfin aljihun sa. Abinda ya rage masa shine idan ba zai iya ba sai dai ya tafi gefen gari inda babu abubuwan more rayuwa ko kuma ya tsallaka zuwa Suleja ko Keffi, nan kuma zai yi ta jigila da kudin mota.
Bangaren zamantakewa kuma, duk mutumin da yake aiki ko sana’a a Abuja, a garinsu ko kauyensu ana masa kallon ya haye. Duk ranar da aka ce ya zo ganin gida to ‘yan uwa da abokan arziki na nan na jiran sa da bukatu iri iri kowa yana so ya ya gi nasa rabon, sai ka ga mutum ya fara wasan buya da mutane.
Akwai wani batu mai muhimmanci da ya kamata a taba a wannan rubutu. Wannan kuwa shi ne irin takun sakar da ke tsakanin masu tallan kaya a hanya ko masu kasa kaya a gefen hanya da kuma hukumar kula da muhalli ta birnin Tarayya wato AEPB.
Wadannan masu sayar da kaya suna gudanar da cinikayyarsu ne kullun cikin dari-dari. Yanzu kana iya ganin su suna ciniki hankali kwance an jima kadan kuma ka gan su suna ta guje guje da kayansu a ka. Mafi yawan masu wadannan san’o’in su ma ba haka suka so ba, kuma za ka ga suna da burin a ce ina ma za a samar musu da wani wuri kebabbe da za su gudanar da cinikinsu ba tare da tsangwama ba.
0708 762 6989