Bello Hamza" />

Birtaniya Ta Samar Da Hanyar Rabuwar Aure Ta Kafar Sadarwar Intanet

Kiev, Ukraine - October 17, 2012 - A logotype collection of well-known social media brand's printed on paper. Include Facebook, YouTube, Twitter, Google Plus, Instagram, Vimeo, Flickr, Myspace, Tumblr, Livejournal, Foursquare and more other logos.

kasar Birtaniya ta samar da kafar shigar da takardar neman kashe aure ta hanyar kafafar sadarwa na zamani wato (Intanet) garin Ingila da Wales saboda a sauwaka wa jama’a hanyar rabuwar aure.

Ma’aikatar Shari’a ce, ta sanar da haka, ta ce, tuni aka samar da hanyar shigar da bukatar rabuwar aure ta kafar sadarwa tun daga wannnan watan na Mayu.

Ma’aikata shariar ta ce, wannan tsarin zai kawo karshen wahalhalun dake tattare da shigar da bukatar neman kashe aure ta hanyar amfani da takarda.

An tabbatar da cewar, tsarin yana da saukin gaske, ta yanda za a iya kamala sukkan cike cike ba tare da wani wahala har da biyan kudade da kuma shigar mika hujjojin da ake bukatar gabatarwa tun kafin a shiga zaman kashe auren.

Ma’ikatar ta ce, an isar da korafe korafe har 1,000 ta wannan sabon tsarin, inda aka lura da cewa, a cikin duk korafi 10 suna nuna amincewarsu da wannan sabon tsarin suna kuma nuna gamsuwarsu.

Ma’aitan shari’ar ta kara da cewa, a halin yanzu yana daukar ma’aikatansu awannin 13,000 wajen yin nazarin takardun bukatar neman kashe aure, wannan sabon tsarin ya kawo mana saukin fiye da kashi 95,an kuma samu raguwar mayar da takardar neman sakin saboda kurakuran da ake yawan tafkawa a lokuttan baya.

Ministan sharia Lucy Frazer, ta ce, “Mika takardar neman saki ta kafar sadarwa zai tabbatar da mun zama mutanen dake kasancewa tare da juna da kuma tallafawa juna a kowanne lokaci.

“Mutane da dama zasu shiga wannan tsarin dake da saukin gaske yana kuma rage asara ya kuma yi daidai da wannan zamanin da muke ciki”

A nasa tsokacin, shugaban kotun iyali, Sir James Munby, ya ce,“Wannan tsari na neman bukatar saki ta kafar sadarwa intanet ya samu gaggarumin nasara, hakan kuma yana nuna inda aka nufa ne à yan shekaru masu zuwa”

Wannan sabon tsarin yana cikin Dala Biliyan 1.4 da gwamnatin Amurka ta samar domin sake fasalin kotunan kasar, hakan kuma zai kara kusantar da tsarin ga jama’a, yana kuma da saukin gaske.

An bayar da misalin wata mai suna Rebecca, wanda ta yi amfani da wannan tsarin ta kuma samu sakon tabbatar da mutuwar auren ta a cikin mako 12 kacal.

Wata kuma mai suna Elaine Eberett, da ta rabu da mijin nata har na tsawon shekara biyu kafin tayi amfani da wannan tsarin wajen neman mutuwar auren nata ta ce, “Lallai tsarin nada matukar amfani, babu wahala babu wani rikici, “Lallai na ji dadin tsarin kwarai da gaske” inji ta.

Exit mobile version