Gwamnatin Birtaniya ta tsaida wasu kasashen Afirka 11 shiga kasarta na tsawon makonni biyu.
A cikin wata sanarwar da ta wallafa a shafinta na intarnet, gwamnatin Birtaniyar tace ta dauki matakin ne don dakile cigaba da yaduwar sabon nau’in cutar korona da ta samo asali daga Afrika ta Kudu.
Kasashen da Birtaniya ta hana zirga-zirga tsakaninta dasu sun hada da Nambia, Zimbabwe, Zambia, Malawi, Angola, Lesotho, Eswatini, Bostwana, Maurituis, Seychelles da kuma Mozambique, ba ya ga Afrika ta Kudu da tuni ta dakatar da zirga-zirga tsakaninsu.
Rahoton ma’aikatar lafiyar Birtaniya a ranar Juma’a sun nuna cewar akalla mutane 1,350 annobar korona ta halaka a kasar cikin sa’o’I 24, adadi mafi muni da kasar ta gani tun bayan bullar cutar cikin kasar sama da shekara guda.