Bisa Kuskure: Jirgin Yaki Ya Farmaki Sojoji A Borno

Sojin Sama

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri

Majiyar sojoji ta bayyana yadda bisa kuskure jirgin yaki ya farmaki motar sojojin Nijeriya a sa’ilin da ya ke kokarin kai dauki a harin Mainok, da ke jihar Borno.

Jirgin sojan sama, bisa ga kuskure, a lokacin da yake kokarin auna mayakan Boko Haram, ya farmaki motar sojojin wanda hakan ya yi sanadin mutuwar wasu daga ciki da dama.

A bayanin Diraktan hulda da jama’a na rundunar sojojin sama ta Nijeriya, Air Commodore Edward Gabkwet, ya ce ba su tabbatar da batun ba har sai sun kammala bincike kan lamarin.

Edward ya bayyana hakan a shafin rundunar sojan sama na Tweeter ranar Litinin ya ce suna ci gaba da gudanar da bincike kan wannan zargin kana kuma daga baya zasu sanar da yan Nijeriya sakamakon binciken faruwar lamarin a garin Mainok mai tazarar kilomita 55 daga Maiduguri.

Bugu da kari, yan kungiyar Boko Haram sun kai harin ne a sansanin sojoji da ke garin Mainok tare da mamaye wajen lamarin da ya tilasta sojojin neman dauki.

Diraktan hulda da jama’a na rundunar sojojin Nijeriya, Brigadier Janar Mohammed Yerima, ya ce yana kokarin bincike dangane da al’amarin- a lokacin da aka nemi jin ta bakin shi.

Exit mobile version