Farfesa Muhammad Babangida Muhammad">

Bitar Littafin Fassarar Tafsirin Ibn Kathir Na Malam Aliyu Ibrahim S/Mainagge

Bitar littafin Fassarar Tafsirin Ibn Kathir na Malam Aliyu Ibrahim S/Mainagge daga Farfesa Muhammad Babangida Muhammad (Daraktan Cibiyar Nazarin Al-kurani Ta Jamiar Bayero, Kano) a taron kaddamar da littafin da a ka gabatar ranar Asabar 20 ga Yuni, 2020 a yanar gizo ta hanyar amfaani da manhajar Zoom.

Auzu billahi minash-shaidanir Rajim. Bismillahir Rahmanir Rahim
Alhamdulillah! Wassalatu wassalamu ala nabiyyina Muhammad, wa ala alihi wa sahbihi ajmain.
Amma baad. Manya-manyan jagorori, shuwagabanni, malamai, da dalibai na ilmi, wadanda suka hadu a wannan guri mai albarka, a wannan dalili mai albarka, game da Alkurani mai girma, ina sallama a gare ku, Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Da farko ina godiya ga jagororin gabatar da wannan littafi, da suka sanya ni a matsayin wanda zai yi bitar wannan gagrumin aiki da dan uwa Malam Aliyu ya gabatar na fassara Tafsirin Ibn Kathir, mafi ingancin Tafsiri wanda Imam Abul Fida ya rubuta, littafi ne wanda hakika yake da muhimmanci da faida kwarai da gaske. Shi Ibn Kathir yana daga cikin manya-manyan malamai magabata, ya rayu a karni na takwas na hijirar Manzon Allah (SAW), an haife shi a shekara ta dari bakwai da daya (701), ya rasu a shekara ta dari bakwai da sabain da bakwai (777).
Littafi ne da yake da kima matuka da gaske da aka gina shi a mafi kyawon madogara, a bisa hasken ayoyin Alkurani, watau Tafsiril kuran bil kuran, sannan da dogaro da Hadisan Manzon Allah (SAW), sannan da maganganun Sahabbai da Tabiai. Ga wanda yake neman tafsirin Alkurani tsantsa, ba tare da surkullen masu labarai na tastuniya da Israiliyyawa ba, to, ya nemi Tafsirin Ibn Kathir.
dan uwan Malam Aliyu Ibrahim S/Mainagge a bisa ilhama da taufiki da Allah (SWT) ya ba shi, ya dukufa watau wajen fassara wannan littafi da harshen Hausa. Aiki ne wanda ya rungumo shi, asali wanda da ya shawarci wadansu da farko, laalla da sun karya masa gwuiwa, su ce da shi kai! Fassarar Tafsirin Ibn Kathir gabaki dayansa? Ba ma Mukhtasar din sa ba? kuma Mukhtasar din sa yana da yawa. Amma Allah (SWT) ga shi ya bawa wannan dan uwa kwarin gwuiwa, da kuma hazaka da jajircewa, yadda ya iya fassara wannan littafi. Allah (SWT) ya saka masa da alheri. Hakika dan uwa Malam Aliyu ya yi gagarumin kokari, abin yabawa, abin san barka, wanda izuwa yanzu ba a san dai wani wanda ya yi makamancin haka ba a harshen Hausa. Madallah da wannan hidima ga Alkurani.
Na karanta takarizi da manya-manyan malamai suka yiwa wannan fassara, cikinsu har da malami na Sheikh Ibrahim Khalil da saoi na Modibbon Gusau Malam Aminu Aliyu da Sheikh Muhammad Ibn Uthman da Dr. Ibrahim Maibushra da Dr. Sani Musa Ayagi, tare da karfafawar gwuiwa da mawallafin ya samu daga iyayenmu Babban Limamin Kano Emeritus Farfesa Muhammad Sani Zaharaddeen da Babanmu Farfesa S.A.S Galadanci Ambasada Murshid, da Farfesa Auwal Abubakar, da sauran sassan malamai da dama, duk wannan yana nuna cewa, lallai wannan dan uwa ya sami dacewa a cikin wannan gagarumin aiki.
Na bibiyi wannan fassara, kuma na iske fassara ce mai kyau, wadda za a iya saukin fahimta, kuma wadda ta dace da kaidojin rubutun Hausa, tare da cewa, wasu gurare salon rubutun larabci ya kan fizgi fassarar Hausar, amma dai maana ta kan fito yadda za a fahimta, ba tare da wahala ba.
karin abin shaawa shi ne bugun littafin an yi shi ya fito tas, yadda zai yi dadin karantawa, babu cakuduwa ko shafewar tawada, ko sarkafewa tsakanin wannan shafi zuwa wannan shafi.
Kamar yadda mawallafin ya fadi, akwai yan kananan gyare-gyare da ba za a rasa ba, littafin Allah ne shi kadai ya tsira daga kuskure. Yan kananan kusakuran nan ba su kai matsayin da zasu rage wani abu ba a kimar wannan littafin. Iza balagal mau kullataini, lam yahmilul khabsa.
Babban abin kayatarwa shi ne yadda mawallafin ya bi diddigin hadisan da Ibn Kathir ya kawo, kuma ya tabbatar da matsayinsu, ko dai na inganci ko kuma rashin inganci, ya yi kuma haka ba da ka ba, ba daga gare shi ba, ya dogara da malamai, masana a wannan fannin, irinsu Sheikh Albaniy da sauransu, hakika wannan shi ma zai kara taimakawa mai karatu ya fahimci madogarar Ibn Kathir.
Ba shakka wannan littafi na wannan dan uwa namu, littafi ne da kowanne musulmi mai jin harshen Hausa ya cancanta ya mallaka, kuma ya karanta domin samun ingantacciyar fahimta ta Alkurani. Babu bangaranci a cikinsa, babu son zuciya, babu karkata, babu son zuciya, sai tatacciyar fassarar maganar Ubangiji, akan hujjoji tabbatattu.
Hakika ko nawa farashin wannan littafi ya kama bai yi tsada ba, mai babur ko mota idan ya rasa kudi, ya sayar da babur din nasa, ko ya sayar da motar domin ya mallaki wannan littafi. Wanda ya tara kayan toshi, ya sayar da kayan toshin domin ya sayi wannan littafin, shi ma bai yi asara ba, Allah (SWT) zai bude ma sa hanyar auren.
Da a ce za a samu daga cikin mawadata, wanda zai yalwata bugun wannaan littafi domin a sami saukin yada shi a cikin alummar Hausa, Allah (SWT) ya ji kan Khalifa Ishaka Rabiu Khadimul kuran, a irin wannan rana baya kyale hidimar Alkurani ta zama koma baya, Allah ya gafarta masa, Allah ya ji kansa. Allah ya saka masa da alheri.
Malam Aliyu ya sauke nasa nauyi, kuma muna rokon Allah (SWT) Allah ya biya shi da gidan aljanna, saura kuma ya rage ga sauran alummar musulmi wadanda zasu bugi kirji, su duba aljihunsu, su sayi wannan littafi su karanta, da kuma wadanda zasu dauki nauyin buga shi da yada shi a cikin alumma, Allah (SWT) ya taimaka, ya sa albarka.
Wassalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Farfesa Muhammad Babangida Muhammad,
Daraktan Cibiyar Nazarin Alkurani na Jamiar Bayero da ke Kano,
Asabar, 20 ga Yuni, 2020.

Advertisements
Exit mobile version