Biyafara: Da Zubar Da Jinin Da Ake Yi Gwamma A Raba Nijeriya –Shehu Aljan

Daga Mubarak Umar, Abuja

Shahrarren mai kama barayin shanu, ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane, Shehu Musa wanda aka fi sani da Aljan, ya bayyana rikicin biyafara a matsayin wani matakin na gurgunta Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba, a cewarsa, abubuwan da suke faruwa a Kudanci Nijeriya sun sabawa hankalin dan’adam balle a jingina da addini.

Shehu Musa Aljan ya fadin hakan ne a tattaunawarsa da wakilinmu ta wayar tarho, inda ya ce ya kamata mahukunta su dauki matakin gaggawa don magance rikicin na ‘yan biyafara, kar lamarin ya zo ya fi karfin mutane.

Aljan ya ce, ‘yan Arewa suna da hankali kuma suna jin maganar magabatansu, saboda haka babu wani shiri na ramuwa game da cin mutunci da ake yi wa Hausawa mazauna yankunan Inyamuranci. Amma dai akwai bukatar a tsawatar.

“Duk abubuwan da suke faruwa mutane suna gani, ‘yan biyafara suna duka da kashe mutane, suna kuma sanya a kafafen sadarwa kowa yana gani, wannan fadan ba shi da alaka da raba kasa, kawai dai ana son kashe musulmi ne. Mutumin da yake son a raba kasa me ya kai shi kashe mutum ko kona wuraren ibada.” In ji shi.

Ya ce, akwai bukatar Gwamnati ta duba lamarin da idon basira, domin rayukan wadanda ba su ji ba, ba su gani yana salwanta haka kawai. A cewarsa matukar ba a dauki mataki ba, ba a san abinda ka iya zuwa ya dawo ba.

Aljan ya alakanta rikicin biyafara a matsayin sabon salo na tadiye Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, a cewarsa, lokacin da Goodluck Jonathan yake kan mulki babu wanda ya fito yake kashe mutane da sunan kafa kasar biyafara.

Ya ce, kamata ya yi a jinjinawa Buhari bisa kokarin da yake na ganin an magance matsalar Boko Haram, wanda hakan bai yi wa wasu mutane da yawa dadi ba, shi ya sa aka bullo da biyafara don a hana gwamnatinsa tabuka abin kirki.

Har ila yau ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta bullo da hanyoyin magancen wannan balahira cikin ruwa sanyi, domin ita rigima farkonta aka sani ba karshenta ba.

“Wajibi ne ga Gwamnatin Tarayya ta sauya salon magance matsalar biyafara, an tura ‘yan sanda sun kasa, an tura sojoji sun kasa. Yanzu lamari ya koma tsakanin talakawan Hausawa da Igbo, ana bin mutane ana konawa da taya, an rasa wanda zai tsawatar. Da a cigaba da zubar da jini haka gwamma a raba kasar kowa ya kama gabansa.” A cewar Aljan.

Exit mobile version