Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Gwamnan Jihar Bauchi, Alhaji Muhammad Abdullahi Abubakar, ya nuna matukar damuwarsa a bisa yadda wasu jama’ar kasar ne ke daukar tashin hankali ko tada zaune tsaye a matsayin hanyoyin da suke bayyana kukansu ko korafinsu ga duniya, maimakon bin yanyoyin da doka ta tanadar.
Wannan batu ya fito ne a wata takarda da fadar gwamnati ta rabawa manema labarai, inda gwamnan ya ce, “duk wanda bai gamsu da wasu al’auara ba, to akwai hanyoyi da kafafe da yawa wadanda suka dace da zai bi wajen bayyanawa ko gabatar da kokensa ba tare da daukan doka a hanu ko tashin hankali ba.”
“Ina mai nuna matukar damuwata a bisa yadda tashin hankali ya ke faruwa a wasu sassan Kudu Maso Gabashin Kasar nan, wanda ke jawo da fargaba a zukatan dubban jama’a”.
“Yana da kyau ‘yan Nijeriya su guji yin duk wani abun da zai kawo kiyayya da rarrabuwan kawuka a tsakanin al’umma, musamman ta hanyar yada jita-jita da kalaman batanci da tunzurarwa a kafafen yada labarai, musamman ta yanar gizo”.
Gwamnan ya bayyana cewar Nijeriya kasa ce wacce Allah ya hada jama’a mabanbanta a cikinta, saboda haka ya bukaci da a yi hakuri a zauna wuri guda tun da Allah ne ya ga dama ya hada jama’a domin su yi rayuwarsu ta yau da gobe. a cewarsa babu wasu da suke da mallakin wannan kasar illa dai al’umman da suke cikinta.
“A daidai lokacin da Nijeriya take kan farfadowa daga radadin karyewar tattalin arziki, kamata ya yi mu karkata da hankalinmu wajen gina kasarmu ingantacciya. Sabo da haka ba zamu amince wa baragurbi a tsakaninmu ba; suna jefa mu a cikin wasiwasi da kuma tashin hankali”. A cewar Gwamnan.
Gwamnan ya kuma yi kira ga hukumomin da abun ya shafa da su hanzarta daukar matakin da ya dace kan mutanen da suke jawo wa Nijeriya hatsaniya da tashin hankali, a cewarsa yin hakan ne zai magance aukuwar irin wannan a wasu sassan kasar.
Har ila yau, Gwamnan ya jinjina wa al’ummar jiharsa ta Bauchi a bisa yadda suke kokarin tabbatar da zaman lafiya da nuna halin kwarai, inda ya bukaci da si ci gaba da abubuwan da suke yi.
A karshe ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su rungumi zaman lafiya a maimakon tashin hankali domin inganta rayuwa a tsakanin juna.