Biyan CBN Bashin Dala Biliyan 2.1 Zai Durkusar Da Jihohi, Gwamnoni Sun Koka

CBN

Gwamnoni sun tuntubi Gwamnan Babban bankin Nijeriya (CBN) Godwin Emefiele, inda suka roke shi da ya dakatar da shirin fara cire bashin dala biliyan 2.1 na tallafin kudi da gwamnatin tarayya ta ba jihohin.

“Jihohi za su durkushe idan aka dauki wannan matakin. Babban al’amarin shine cewa, jihohi ba za su iya biyan albashi ba. Ma’aikata za su tafi yajin aiki kuma komai zai gurgunta”, inji wani gwamna yayin da yake magana da manema labarai a daren ranar Lahadi.

Emefiele a makon da ya gabata ya ce, dole ne gwamnatocin jihohi su fara biyan bashin tallafin Kasafin kudi da Gwamnatin tarayya ta ba su.

Ya yi magana ne dangane da ikirarin da Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki ya yi na cewa, Gwamnatin tarayya ta buga kimanin Naira biliyan 60 don kara yawan kudin shiga na Maris kafin Kwamitin raba asusun tarayya (FAAC) ta raba shi ga tarayyar, jihohi da kananan hukumomi.

Amma, daga takardar da kungiyar Gwamnonin ta fitar, jimlar kudin shigar da za a rarraba a watan Maris ya kai Naira biliyan 596.94.

Kungiyar ta ce, saboda karancin kudaden shigar da aka samu idan aka kwatanta da watan da ya gabata, an yi karin kudi a kan kudi Naira biliyan 8.65 daga asusun ba da lamuni na ‘Fored’.

Suka ce, karin ya kawo jimlar kudin shigar da za a rarraba zuwa Naira biliyan 605.59.

Binciken da wakilinmu ya gudanar ya nuna cewa mafi yawan gwamnonin sun kadu da shawarar da CBN ta yanke na fara cire rancen dala biliyan 2.1.

An gano cewa baya ga kiran kai tsaye ga Emefiele, mambobin PGF sun shiga cikin rikici da ikirarin da Obaseki ya haifar.

Sanarwar da PGF din ta saka wanda aka sakawa Obaseki ya kasance wani bangare ne na kusantar da CBN don bankin koli zai ci gaba da daukar mataki a kan kudin.

Gwamnonin PDP a jiya sun ba da goyon baya ga Obaseki tare da caccakar Emefiele, suna masu bayyana abin da ya aikata a matsayin ramuwar gayya.

Wani gwamna, wanda ya yi magana cikin amincewa tare da wakilinmu, ya kara da cewa, “Mun riga mun tuntubi gwamnan CBN don dakatar da aiki kan mayar da dala biliyan 2.1. Ya bayyana cewa, matsayin na CBN mataki ne na ramuwar gayya, bayan da’awar Obaseki.

“Babu shakka Emefiele ya fusata saboda Obaseki yana kan matsayin sa na sanin gaskiya. A matakin kungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF), Obaseki da Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ne ke kula da kwamitin da ke hulda da Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) da sauransu. Suna da muhimman bayanai kuma suna da cikakkiyar fahimtar abin da ke cikin hadari. Gudummawar da suka bayar sun taimaka sosai ga gwamnati da mambobin kungiyar Gwamnonin. Fushin ya dogara ne akan gaskiyar cewa Obaseki a matsayin mai sa ido bai kamata ya zama mai tsabta ba. Bai dace da dukkan jihohi 36 da babban birnin tarayya (FCT) ba da damar barin takaddamar ta dore ba,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Muna da kwarin gwiwar cewa, Emefiele zai duba dukkan alkaluman tattalin arziki ya kuma jinkirta mayar da dala biliyan 2.1 zuwa wani lokaci da tattalin arzikin kasar zai murmure sosai daga koma baya. Ya zuwa yanzu, tattalin arzikin yana da rauni kuma jihohi ba za su iya biyan dala biliyan 2.1 da aka basu ba. Karfin ba kawai a wurinmu yake ba. Jimillar kudinmu ya yi daidai da kusan dala biliyan 26. Kasafin kudin shekara-shekara na bangaren noma a kasar Brazil kadai ya kai kusan dala biliyan 56 daga cikin kasafin kudin kasar na kusan dala biliyan 264. Abin da gwamnonin ke cewa shi ne, ya kamata Gwamnatin tarayya da jihohi su hada kai don mayar da tattalin arzikin bisa turba mai madaidaiciya kafin mu fara maganar dawo da dala biliyan 2.1. Dukanmu muna da abubuwa da yawa da za mu yi don sake fasalin tattalin arzikinmu.”

Gwamnan ya ce, bankin na CBN yana sane da cewa kimanin Naira biliyan 120 na Gwamnatin tarayya, jihohi da babban birnin tarayya ana cire su ne duk wata daga kudin da ke cikin asusun tarayya don tallafin man fetur.

Gwamnan ya bayyana cewa, gibi daga FAAC na iya dadewa sai dai idan Gwamnatin tarayya da Jihohi sun hada kai don magance matsalar tallafin mai.

Majiyar ta kara da cewa, “Duk da karin kudin mai, kudaden da ake rarrabawa a cikin asusun na FAAC bai isa ba ga jihohi saboda an cire Naira biliyan 120 mallakar Gwamnatin tarayya, jihohi da babban birnin tarayya duk wata don tallafin man fetur.”

“Mun riga mun biya kusan Naira tiriliyan 1.3 a kowace shekara a matsayin tallafin mai. Wannan yana nufin, kudin da yakamata muyi amfani dasu don manyan ayyuka ana barnatar da tallafin. Duk da haka, da wuya mu cinye kashi 60 na matatun da aka tace. Ana sayar da wasu a cikin kasashe masu ingantattun kasuwanci. Ko dai mun cire tallafin mai ko kuma mu ci gaba da rayuwa tare da tallafi da gibi a cikin kudaden shigar da za a raba su,” ini majiyar.

Exit mobile version