Biyu Sun Mutu, Dan Sanda Ya Bata A Rikicin ’Yan Ci-ranin Anambara

Rahotanni daga Jihar Anambara sun tabbatar da mutuwar mutum biyu tare da bacewar wani dan sanda a wani rikici da ya barke a tsakanin mazauna Odekpe da Allah-Onugwa da ke yankin Karamar Hukumar Anambara ta Yamma a jihar Anambara.

Dan sandan da aka tura domin tabbatar da zaman lafiya a yankin ya bace bat, Rikicin ya barke ne a daren ranar Lahadi a wani sansanin ‘yan ci-rani da ke yankin Igbamaka a shiyyar Ilushi. Tun a cikin watan Yuli aka fara ‘yan kananan rigingimu a tsakanin mazauna garuruwan biyu a kan wasu filaye da ke kan iyakokinsu.

Wani mazaunin Allah-Onugwa, Dabid Uzor, ya ce suna zargin mutanen Odekpe da kai musu hari. “Dumbin mutane daga Odekpe sun dira sansanin da jama’a ke zaman ci-rani. Sun fara harbin ‘kan mai uwa da wabi’ bayan isarsu, sun tarwatsa mutane. “Sun kama dan uwan mahaifina mai suna Anthony Uzor, sun tafi da shi zuwa garin Odekpe inda suka yi masa kisan wulakanci.

Da farko sun datse masa hannaye da kafafu, kafin daga bisani su yi masa yankan rago. “Sun yi zargin cewa mutanenmu sun kashe wani mutumin garinsu, amma daga baya gaskiya ta fito, an gano cewa wani mutum ne daga jihar Edo ya kashe dan uwan nasu a kan wata matsala da ta shiga tsakaninsu,” a cewarsa.

Uzor ya ce maharan sun harbe wani mutumin kauyen Igbamaka, sun raunata mutane hudu, sannan kuma sun lakadawa mata uku dukan tsiya, daga bisani kuma suka dauke musu wayoyi.

Da ya ke mayar da martani a kan lamarin, wani basarake a kauyen Odekpe, Cif Austen Anerah, ya musanta zargin Uzor tare da bayyana cewa mutanen Allah-Onugwa ne suka fara kashe musu wani mutum mai suna Goddy Chukwuemeka. A cewarsa, mutanen garin Allah-Onugwa suna kitsa karya domin jama’a da rundunar ‘yan sanda su tausaya musu. Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Anambara, Haruna Mohammed, a kan faruwar lamarin ya ce rikicin ya faru ne a wurin da kwamand din ‘yan sandan Anambra basu da hurumi da shi.

Mohammed ya shawarci wadanda rikicin ya ritsa da su su tuntubi ofishin rundunar ‘yan sanda mafi kusa da wurin da rikicin ya faru.

Exit mobile version